Mata kar ku karaya a harkar siyasa – Misis Saraya Agidi(1)
amar yadda ya ke a da. Yanzu ko ka rubuta proposal wa gwamnati cewa ta taimake ka za ka ji tana cewa ita kanta ma tana fuskantar rashi. Saboda haka wannan babban kalubale ne da ke ci mana tuwo a kwarya. Amma zan yi amfani da wannan damar in godewa gwamnati mai ci yanzu a […]
amar yadda ya ke a da. Yanzu ko ka rubuta proposal wa gwamnati cewa ta taimake ka za ka ji tana cewa ita kanta ma tana fuskantar rashi. Saboda haka wannan babban kalubale ne da ke ci mana tuwo a kwarya. Amma zan yi amfani da wannan damar in godewa gwamnati mai ci yanzu a jihar nan karkashin jagorancin Umaru Tanko Almakura don a halin yanzu ta sayo mana bus mun kuma samu fili da yanzu muna buga bulok. Mun dade ba mu da ofis, shiyasa ina so in gina ofis din mu na jiha kamin in sauka. Saboda haka a takaice dai kamar yadda na bayyana a baya babban kalubale da muke fuskanta a halin yanzu kenan.
Nasarori da kungiyarmu ta cimma a karkashin shugabanci na
daya daga cikinsu shine kaga tunda a ka kirkiro da jihar nan a shekarar 1996 ba a taba ba mace mukamin sakatariyar gwamnati ba sai a lokacina. Mun kai kukarmu wa gwamna cewa anjima ana yi a gwamnatoti da suka shude banda mu. Muna so ya yi wani abu game da haka. Sai Allah Ya sa kuma shi gwamna Umaru Tanko Almakura ya san darajar mata bai yi wata-wata ba wajen amince da haka inda ya nada Hajiya Zainab Ahmed a matsayin sakatariyar gwamnatin jihar nan. Haka kuma akwai kwamishinoni da daraktoci da dai sauransu da dama mata daya nada a gwamnatinsa na yanzu.
Kafin in zo kungiyar ba ta da mota. Na kai kuka wa gwamnati game da hakan inda ta sayo mana mota bus da ke inganta harkokin kungiyarmu. Kamar yadda na bayyana maka kuma muna da fili da muke shirin gina ofishinmu na jiha. Idan muka fara ko ba mu iya gamawa ba dai wace za ta zo a baya na za ta kammala. Kuma ka ga mata da dama a jihar nan yanzu sun san menene hakinsu a lokacina. Ka ji kadan daga cikin nasarori da muka cimma kenan da ikon Allah.
Shawara ga mata ‘yan’uwana
Kiran da zan yi wa mata ‘yan’uwana kamar kullum shine a bangaren siyasa. Idan ka lura da abubuwa da suka faru a zabubbuka da a ka kammala kwanan nan a fadin kasar nan mata da suka fito takara galibinsu basu samu nasara ba. Amma kada mu karaya da haka. Mu ci gaba da fitowa a duk lokacin zabe mu tsaya takara da haka dai watarana Allah zai ji tautsayinmu ya ba mu nasara. Kar da mu gaji, idan lokacin Allah ya yi babu wanda zai hana mu shugabancin kasar nan a kowanna fanni. Haka kuma mata a rike sana’a da gaske komin kankantarta don dogaro da kai. Mijinki ba zai iya biya miki dukka bukatunki ba. Don idan ya lura kina da sana’a da kina iya taimakawa kanki zai ji dadi ya rinka tallafa miki ya kuma girmama ki yadda ya kamata. Amma idan ya kasance komai kina jira ya yi miki, to ba shakka za ki samu babbar matsala don ba zai ba ki ba ko da yana da shi. Kuma ba zai rinka girmama ki ba maimakon haka sai ya yi maki kallon ke ba komai ba ce. Kuma idan hakan ya faru ba laifinsa bane laifin ki ne don kin ki tashi ki nemi na kanki.