Mata ke binne gawarwaki a Gwoza – Ndume
dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Muhammad Ali Ndume, ya bayyana bakin ciki da damuwa dangane da halin da al’ummomin da ke iyakar Najeriya da Kamaru a karamar Hukumar Gwoza suka samu kansu a ciki, bayan harin da ake zargin Boko Haram da kaiwa a yankin, inda ya ce an bar mata […]

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Muhammad Ali Ndume, ya bayyana bakin ciki da damuwa dangane da halin da al’ummomin da ke iyakar Najeriya da Kamaru a karamar Hukumar Gwoza suka samu kansu a ciki, bayan harin da ake zargin Boko Haram da kaiwa a yankin, inda ya ce an bar mata da aikin binne gawarwakin mutanen da aka kashe a yankin.
Sanata Ali Ndume ya ce jama’ar suna fama da yunwa da tsoro da rashin matsuguni, inda har ta kai mutum 1200, suka yi hijira zuwa garin Maiduguri domin tsira da rayukansu.
Mako biyu ke nan da kungiyar Boko Haram take kai hari a yankin Gwoza, a gundumomi shida da suka hada da Attagara da Agafalawa da Ngoshe da Fulka Boko da Cikide da Kuhum inda suka kashe mutanen da yawansu ya haura 100 da kone gidaje da kasuwanni da dabbobi, tare da warwason abinci su yi gaba dashi, abin da ya jefa mazauna garuruwan cikin mawuyacin hali.
Sanata Ndume, ya nemi taimakon gwamnati da kungiyoyi da daidaikun jama’a su tallafa wa ’yan gudun hijirar, inda ya ce “Mutanenmu sun shiga cikin mawuyacin hali na rashin abinci da matsuguni sakamakon harin da ’yan bindiga suka kai a gundumomin Attagara da Agafalawa da Ngoshe da Fulka Boko da Cikide da Kuhum, an rasa rayukan sama da mutum 100, da tilasta mutum 1200 yin gudun hijira, mata kawai aka bari a garuruwan suna aikin binne gawarwaki.”
Sanata Ndume ya ce ko kadan ba fadan addini ba ne, makiyinsu Boko Haram ne ba wai fada ne tsakanin Musulmi da Kirista ba. Ya bukaci jami’an tsaro su gaggauta zuwa garuruwan domin kubutar da mutanensu saboda har yanzu suna cikin tsaka-mai-wuya, kuma maharan suna can a garuruwan suna barna.
Su kuwa shugabannin gundumar Attagara Abba Kaka, mai wakiltar Musulmi da John Gula, mai wakiltar Kiristoci, sun nuna bakin cikinsu dangane da harin da ’yan bidigar suka kai musu, kuma sun karyata jita-jitar cewa wannan hari na addini ne. Kuma sun tabbatar ce mata ne ke binne gawarwaki a bayan dutse da dazukan da ke yankin.