Mata ke jawo almundahana a Najeriya – Jummai Bello
Wata wakiliya a wurin Taron kasa mai suna Jummai Bello ta ba takwarorinta mata mamaki, lokacin da ta soki mata da jawo almundahana da cin hanci a Najeriya. Malama Jummai Bello, wadda wakiliya ce da ta fito daga kungiyar Manyan Ma’aikata (TUC) ta bayyana haka ne lokacin da take tofa albarkacin bakinta kan jawabin da […]
Wata wakiliya a wurin Taron kasa mai suna Jummai Bello ta ba takwarorinta mata mamaki, lokacin da ta soki mata da jawo almundahana da cin hanci a Najeriya.
Malama Jummai Bello, wadda wakiliya ce da ta fito daga kungiyar Manyan Ma’aikata (TUC) ta bayyana haka ne lokacin da take tofa albarkacin bakinta kan jawabin da Shugaban kasa ya gabatar wajen bude taron, inda ta ce da mata suna sauke nauyin da ke kansu na kula da gida yadda ya kamata da Najeriya ba ta fuskanci bala’in almundahana da rashawa ba.
Ta ce matan Najeriya sun gaza ba ’ya’yansu tarbiyyar da ta kamata, kuma su suke karfafa wa mazajensu suna aikata almundahana da cin rashawa.
Malam Jummai ta ce wasu iyaye mata kan karfafa gwiwar ’ya’yansu a lokacin da suka ga suna sayen abubuwan da suka fi karfinsu. Kuma a cewarta, maimakon su rika hana mazajensu gudanar da rayuwar da ta fi karfin samunsu ko sayen motocin da albashinsu ba zai iya ba, wasu matan ma kan rika misali ga mazajensu da na makwabta ne, lamarin da ke ingiza su su yi almundahana.
“Wajibi ne mu fada wa kanmu gaskiya, mata ne tushen matsalar da muke fuskanta a kasar nan. Ba mu tarbiyyantarwa ko renon ’ya’yanmu yadda ya kamata. Don haka wajibi ne mu yi kokarin ikonmu wajen tabbatar muna kula da ’ya’yanmu yadda ya kamata,” inji ta.
Ta kawo misali da yadda ta taso, inda ta ce a wancan lokaci a matsayinta na yarinya, idan ta kawo wani abu da ba nata ba zuwa gidansu, iyayenta za su kwace kuma su yi mata duka.
Jummai Bello ta yi nadama kan yadda al’amarin ya sauya a yanzu ta yadda a yanzu iyaye ne ke karfafa gwiwar ’ya’yansu idan suka kawo sabon abu cikin gidansu.
Malama Jummai, wadda ta rika shan tafi a lokacin da take jawabin, ta koka kan yadda a yanzu mata ke satar kudin gwamnati a ofisoshinsu. “Ban taba mafarkin cewa mata za su iya satar kudin gwamnati ba, amma sai ga shi suna yin haka a yanzu. Wajibi ne mu canja dabi’unmu,” inji ta.