Mata ku kariya ga mazajenku -Malama A’ishatu Muhammad Kyaftin

Malama A’ishatu Muhammad Kyaftin ita ce Mataimakiyar Magatakarda (Deputy Registrar) A Kwalejin Horar da Malamai FCE da ke Zuba ta Abuja.  Ta bayyana fadi-tashin da ta sha a rayuwarta sannan ta yi kira ga mata da su daina shiga harkar siyasa kuma hakan ce ta sa wasu matan suke yi mata kallon mai tsattsauran ra’ayi. […]

Mata ku kariya ga mazajenku -Malama A’ishatu Muhammad Kyaftin
Mata ku kariya ga mazajenku -Malama A’ishatu Muhammad Kyaftin

Malama A’ishatu Muhammad Kyaftin ita ce Mataimakiyar Magatakarda (Deputy Registrar) A Kwalejin Horar da Malamai FCE da ke Zuba ta Abuja.  Ta bayyana fadi-tashin da ta sha a rayuwarta sannan ta yi kira ga mata da su daina shiga harkar siyasa kuma hakan ce ta sa wasu matan suke yi mata kallon mai tsattsauran ra’ayi.  Wakiliyarmu ta samu tattaunawa da ita a batutuwa da dama, ga yadda hirar da kasance:

Tarihin rayuwata: 

Sunana Malama A’ishatu Muhammadu Kyaftin (Captain). An haife ni a garin Kaduna. Na fara karamar makaranta a Saint Micheal, daga nan na koma Turaki a Sakkwato. Bayan na kammala wannan karatu sai na wuce babbar Sakandaren gwamnati ta ’yan mata da ke garin Illela. Sannan na yi karatu a Kwalejin Horar Da dalibai da ke Jihar Sakkwato. Daga nan na tafi bautar kasa (NYSC) a Jihar Ribas. Daga nan na fara aiki a Jihar Neja a matsayin malama bayan haka ne na je na yi digiri dina, a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno. Bayan haka sai na fara aiki da Kwalejin horar da dalibai da ke Zuba ta Abuja kuma har na kawo wannan matsayi na Mataimakiyar Magatakarda(Deputy Registrar).
Ta fanin rayuwa kuwa na yi aure ina da yaro guda da Allah Ya albarkace ni da shi, sannan ban da shi ina rainon wadansu yara marayu.
Me ya ba ki sha’awar yin wannan aiki?
Saboda ta wannan hanyar nake son in bada tawa gudumawa wajen taimakawa al’umma don a samu cigaba mai dorewa.
Me za ki ce game da koma bayan ilimin mata?
Abin da ya sa tun farko kakanninmu sun nuna ilimin mata ba dole bane abin da ya fi dacewa da mace shi ne ta yi aure. A wancan lokaci shi ya sa ba su damu da sanya mata a makaranata ba, sannan suna ganin ’ya mace sai an yi kaffa-kaffa da ita don gudun abin da ke iya faruwa. Wannan tsoron ne ya sanya ba sa barin ’ya mace ta fita ma balle a kyaleta ta je makaranta. Da sannu har kai ya fara wayewa suka ga mahimmancin maarantar aka fara barin su suna shiga makaranta amma duk da haka an fi ba da karfi ga maza. To tushen wannan matsala ta samun koma bayan ilimin mata a yankin Arewa ke nan. Na biyu kuma idan mace ta yi aure yawanci ba a barin ta je ta kara neman ilimi sai a bar ta nan gida kawai, wanda yin haka bai kamata ba, samun ilimin boko da Islamiyya yana da muhimmanci kwarai don ta wannan hanya ce kadai mace za ta iya kula da mijinta da kuma tarbiyar ’ya’yanta.
Mene ne burinki a rayuwa:
To ni burina sh ine in ga na canza rayuwar mata don su gane mahimmacin addininsu a kowane hali suka sami kansu saboda na lura yawancin mata idan suka sami llimin boko mai zurfi ba su cika kula da dokokin addinin Islama ba. Za ka tarar ba su cika yin shiga irin ta Musulunci ba ta hanyar sanya Hijabi, wannan ta sa kullum nake kira da lallai mata su rike mutuncinsu ta hanyar bhin dokokin adinin Islama sau da kafa. Yau an wayigari wai matan Musulmi ne da kansu suke kyamar sanya hijabi. To wadanda ba Musulmi ba idan suka gane haka ai ka ga akwai matsala, za su yi mana dariya ne kawai. Don haka burina shi ne kowace mace, ta maida hankalinta kan karatun addini da kuma yin aiki da duk abin da ta sani domin tsira daga azaba. Allah Ya gafarta mana Ya karbi ibadarmu kuma Ya kara mana karfin imani. Don haka ina kira ga mata mu zama kariya ga mazajenmu, mu taimaka musu wajen nisantar haramun don yawancin hadarin da mazaje ke sa kansu mata ne ke janyo musu, don haka dole ne mu rika yi wa mazajenmu wa’azi a kullum don mu tsira don haka nake son na canza rayuwar mata zuwa ga hanya mafi dacewa.

Mene ne ya fi bata miki rai?

Babban abinda ya fi bata mini rai shi ne in ga Musulmi yana jayayya da abin da aka ce Allah Ya ce. Wannan bai dace ba sam-sam.
Mun ga kina da burin taimaka wa mata, wadanne hanyoyi ki ke bi don cimma wannan buri?
Ina da kungiyar da nake amfani da ita wajen tallafa wa al’umma, musamman mata da yara da kuma marasa galihu. Sannan mata irinmu masu hali mun kafa kungiyoyi daban-daban da ke tallafa wa gajiyayyu da marasa galihu. Yanzu haka mun yi nisa wajen aiwatar da irin wadannan abubuwa kuma cikin yardar Allah muna samun nasarori.
Wadanne hanyoyi kike ganin idan an bi za a gyara al’umma?
Da farko dai a ji tsoron Allah, a dogara ga Allah, a bi dokokin Ubangiji shi ne komai.
Me za ki ce game da siyasar mata a kasar nan?
Ni a kullum ina yin kira ne ga mata da su nisanci shiga harkokin siyasa. A matsayinmu na mata bai dace a ce a ganmu kullum muna cudanya da maza wai da sunan yin siyasa ba. Hakan ta sa a kullum mata suke sukata wai ina da tsauttsauran ra’ayi ni kuma na san illar shiga harkokin siyasa ga mata a kasar nan ya fi alfanunsa. Mun sani shugabanci na maza ne, mu mata mu tsaya a matsayinmu na iyaye mu kula da hakkokin mazajenmu. Mu tsaya wurin da Allah Ya ajiyemu kada mu wuce gona da iri. Don haka ni ban goyi bayan mata su rika shiga harkokin siyasa ana damawa da su ba.