Mata ku rage zafin kishi!
Har yanzu ban yarda cewa mata sunfi maza kishi ba, sai dai a iya cewa su maza sunfi mata juriya, su kuma mata sun fi maza iya nuna tabargaza da wauta wai duk da sunan kishi, shiyasa ma ake yimasu kirari da “KISHI KUMALLON MATA”. Shin mene ne kishi? Ya ake yin kishi a Shari’a? […]
Har yanzu ban yarda cewa mata sunfi maza kishi ba, sai dai a iya cewa su maza sunfi mata juriya, su kuma mata sun fi maza iya nuna tabargaza da wauta wai duk da sunan kishi, shiyasa ma ake yimasu kirari da “KISHI KUMALLON MATA”. Shin mene ne kishi? Ya ake yin kishi a Shari’a? Da yawan matanmu na yanzu ko dai ba su da amsoshin wadannan tambayoyi, ko kuma sun sani amma suke take sani.
Muna da tarihin cewa matan Annabawa da Sahabbai sun yi kishi, sai dai abin tambaya a nan shi ne: Shin irin kishin da wadancan matan suka yi, irin shi ne matan mu na yanzu ke yi? amsa anan itace a’a. Abin da wasu matan yanzu keyi da sunan kishi sam sam baza a iya kiran shi kishi ba, sai dai a kira shi da abin tir da Allah wadai.
Abu na farko da wasu mata ke yi na ganin cewa mazajen su ba su samu damar yi masu kishiya ba ita ce sukan gayawa mazajen nasu karara da cewa idan dai don wadata ce ke sawa a karo musu abokiyar zama. To Allah ya bar mutum cikin talauci da wahala, ta yadda ba zai samu damar kara aure ba. Ko sun manta da Allah ne ya umurce mazan da yin haka idan dai har suna da hali, kuma za su iya yin adalci? Wasu matan kan bi hanyar ’yan tsubbu da bokaye (wa’iyazubillah) wai don su samu biyan bukatun su na kada a yi musu kishiya. Idan ba su samu biyan bukata ba a wannan bangare, sukan yi kokarin nakasa mazajen nasu, wani lokacin abin na wuce wa ga kisa, wai duk don kada a samu damar karo musu abokiyar zama (kishiya). Shin idan Allah ya baki yaya mata ashe kina iya cewa diyar ki ba za ta auri mai mata ba? idan kuma ba ki taba aure ba kuma kika ce baki auren mai mata, Shin baki yin tunanin cewa kila matan mahaifinki ba mace daya bace ba? ya kamata ace ko wace mace takan tuna irin wannan amsoshin tambayoyin kafin kokarin aikata wani abu wanda bai dace ba da sunan kishi.
Abun bai tsaya nan ba, wasu matan masu kishiyoyi sukan shiga su fita ta kowace hanya don suga sun raba abokan zaman su da gidan aure, Haba iyayen mu mata ashe lokacin da za ki aikata irin wannan danyen aiki ba ki yi tunanin ko kina da diya wani guri, inda ita ma za a iya yi mata haka ba? Babban abin takaici da Allah wadai da mata ke aikatawa, shi ne yadda zafin kishinsu ke sauka ga yaran da ba su suka haifa ba.
“’da dai na kowa ne kuma ba a san mai amfanar sa ba.” Idan zafin kishi ya sa kika azabtar da dan da ba ke kika haifa ba, to ki sani hakan abin tambaya ne a ranar gobe kiyama, kuma yaron da kike ganin bake kika haife shi ba to akwai yiwuwar ya fi amfana maki bisa ga ’ya’yan da kike ganin kin haifa.
Kuma ashe ba ki tunanin sauyi na rayuwa ko mutuwa ta sa ke ma ki bar wa wasu ’ya’yan naki da kika Haifa, kamar yadda ke ma aka bar miki? Ashe ba ki tunanin abin da kika yi wa dan wani ke ma za a iya yi wa ’ya’yan naki? Mata ku ji tsoron Allah, ku san yadda za ku yi kishi daidai da shari’a. Allah ya ba mu ikon gyarawa dukkan kura-kuren mu baki daya amin.
Habib ya rubuto makalarsa daga Katsina 07038653949 [email protected]