Mata ku shiga a dama da ku a harkar siyasa – Misis Lydia Attah
Misis Lydia Attah ita ce Shugabar Kungiyar Mata Kiristoci (WCAN) reshen Jihar Nasarawa. A tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana ayyukan kungiyar da nasarorinta da sauransu: Ya za ki bayyana harkokin kungiyarku a jihar nan? Babbar manufa ko harkokin kungiyarmu a takaice dai shi ne mu tabbatar da hadin kai da ci gaban addinin Kirista […]
Misis Lydia Attah ita ce Shugabar Kungiyar Mata Kiristoci (WCAN) reshen Jihar Nasarawa. A tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana ayyukan kungiyar da nasarorinta da sauransu:
Ya za ki bayyana harkokin kungiyarku a jihar nan?
Babbar manufa ko harkokin kungiyarmu a takaice dai shi ne mu tabbatar da hadin kai da ci gaban addinin Kirista a tsakanin mata Kiristoci da sauran al’ummar jihar nan baki daya wato wadanda ba Kiristoci ba. Wannan shi ne takaitaccen ayyukan kungiyarmu.
Ya ya dangantakar kungiyarku da ta takwararku mata Musulmi a Jihar Nasarawa?
A gaskiya akwai kyakkyawar dangantaka a tsakanin kungiyarmu da ta su don a koyaushe muna aiki tare ne wajen ganin cewa mata sun samu duk wani hakki nasu wato muna kwato musu hakkinsu a kowane lokaci.
Misali a lokacin tashin hankalin da aka fuskanta a cikin jihar nan, kwanakin baya kungiyarmu da takwararta ta mata Musulmi wato FOMWAN mun hada hannu inda muka kai kukan mata da yara da lamarin ya shafa ga gwamnati aka kuma taimaka musu daidai gwargwado. Mun kuma ziyarci sansanin ’yan gudun hijira inda muke tallafa wa mata Musulmi da na Kiristoci wadanda lamarin ya shafa. Ga kuma ziyartar gidajen marayu da sauransu. Dukan wadannan wurare da ma wasu muna kai irin wadannan ziyarce-ziyarce ne tare da hadin kan kungiyoyin biyu wato na Musulmi da na Kirista saboda akwai kyakkyawar dangantaka a tsakaninmu.
Me kungiyarku ke yi wajen tabbatar da kyawawan dabi’u a tsakanin al’umma baki daya?
A gaskiya muna yin iya kokarinmu wajen tabbatar da kyawawan dabi’u a tsakanin al’ummar jihar nan baki daya.
Babban abin da muke yi shi ne addu’a. Don ka ga ba za ka iya hana wadannan abubuwa da ikonka ba sai ta addu’a don Allah Ya kawo mana dauki. A wasu lokuta kuma mukan gudanar da taron bita inda muke hada kai da mata Musulmi mu ziyarci wurare daban-daban don mu ilimantar da jama’a musamman mata da matasa game da muhimmancin kasancewa masu kirki a cikin al’umma.
Muna gaya musu cewa idan kina da kyakkyawan tarbiyya al’umma za ta yi alfahari da ke. Amma idan kika wulakanta kanki mutane ba za su girmama ki ba. Kuma wannan ziyara muna kaiwa ne a dukan kananan hukumomin jihar nan don Allah Ya magance mana wadannan matsaloli da suka addabi al’ummanmu. Saboda haka muna yin iya kokarinmu daidai gwargwado a wannan bangare kuma za mu dore da haka da yardar Allah don hakki ne da ya rataya a wuyanmu.
Kuna da shiri na musamman ga mata a kan yadda za su tarbiyyartar da ’ya’yansu?
Babu shakka a wasu lokuta mukan gudanar da tarurruka ga mata dangane da yadda za su tarbiyyantar da ’ya’yansu yadda ya kamata. Kamar yadda ka sani idan ba ka koya wa yaro yadda ake yin addu’a da sauransu ba, yaron zai fuskanci matsala a rayuwarsa. Shi ya sa mukan gayyaci yara wajen tarurrukanmu a kananan hukumomi inda muke koya musu yadda za su gudanar da tarbiyya tagari da zai taimaka wa rayuwarsu.
Yaya matsayin mata a harkokin siyasar Jihar Nasarawa musamman a yanzu da zaben 2019 ke gabatowa?
A gaskiya muna ba su shawarar su rika shiga harkokin siyasa ana damawa da su kodayake ni ma’aikaciyar gwamnati ce, an hana mu shiga harkar siyasa amma matanmu da ke siyasa suna samun ci gaba sosai a wannan bangare. Misali mata irin su Mary Enwogulu ta kasance mamba a Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa. Bayan wannan ta taba yin takarar Majalisar Wakilai amma ba ta samu nasara ba. Kuma har yau tana cikin siyasa don kamar yadda ka sani a yanzu ita ce Kwamishinar Ma’aikatar Harkokin Mata a jihar nan. Misis Mary Kigbu tsohuwar Kwamishinar Ma’aikatar Harkokin Mata da Misis Agule ita ma ta yi Kwamishina a jihar nan da sauransu.
Akwai kuma ire-irenta mata a jihar nan da dama da lokaci ba zai ba ni damar bayyana su daya bayan daya ba. Ina so in bayyana maka cewa ana ji da su a harkar siyasa a ciki da wajen jihar nan baki daya. Ina kuma so in yi amfani da wannan damar in nanata kirana a gare su (mata) cewa su ci gaba da fafatawa a harkar siyasa don mu samu damar kwato wa kanmu ’yanci. Saboda haka zan iya cewa mu mata muna samun ci gaba a harkar siyasa a hankali ba a jihar nan kadai ba har da kasa baki daya. Kuma ina tabbatar maka da cewa za a wayi gari wata rana mata ne za su samu rinjaye a shugabancin jihar nan da ma kasa baki daya a dukan fannnonin rayuwa.