Mata ku tashi ku nemi ilimi – Larai Baba

  Hajiya Larai Baba ita ce  Janar Manaja na  gidan Rediyon Unity FM da ke garin  Jos, babban birnin Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ta yi da wakilinmu ta bayyana yadda ta fara aikin jarida, tun tana da shekara hudu a duniya. Haka kuma ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha a aikin rediyo […]

Mata ku tashi ku nemi ilimi – Larai Baba
Mata ku tashi ku nemi ilimi – Larai Baba

 

Hajiya Larai Baba ita ce  Janar Manaja na  gidan Rediyon Unity FM da ke garin  Jos, babban birnin Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ta yi da wakilinmu ta bayyana yadda ta fara aikin jarida, tun tana da shekara hudu a duniya. Haka kuma ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha a aikin rediyo tare da irin nasarorin da ta samu. Daga nan kuma ta bukaci mata kan su tashi su nemi ilimi.

Tarihina: Sunana Hajiya Larai Baba, kuma ni ce Janar Manaja na Gidan Rediyon Unity FM da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato.  An haife ni ne a garin Kaduna. Na yi makarantar firamare a  Kaduna, kuma na yi makarantar sakandare a garin Jos, daga nan na shiga Jami’ar Jos, inda na karanta fannin harkokin watsa labarai. Tunda farko da ma mahaifiyata ta yi aikin jarida a gidan Rediyon Jihar Kaduna, tun  ana kiran gidan rediyon NBC.  Ta yi shekara 35 tana aiki a wannan gidan rediyo, kafin ta yi ritaya.

A lokacin da nake makarantar firamare ina da shekara hudu ina  bin mahaifiyar tawa, zuwa wajen aiki. Tun daga wannan lokaci na fara sha’awar aikin jarida. Daga nan na soma gabatar da wani shiri mai suna ku matso yara da wasu mata  Hajiya Hasana Umar da   Hajiya Hannatu Ibrahim.
Da na gama makarantar firamare na shiga makarantar sakandare, idan aka je hutu nakan je in yi aiki a wannan gidan rediyo, ina  karanta katin zabe da Ingilishi  da gabatar da shirye-shiryen da suka shafi mata da yara.
Da na gama makarantar sakandare, sai na rubuta takadar neman aiki a gidan rediyon na Jihar Kaduna, kuma suka dauke ni. Bayan an dauke ni aiki sai maganar aure ta taso, inda na yi aure a 1977.
Na dawo nan garin Jos a 1978, aka yi mini hanya na fara  aiki da gidan Rediyon Jihar Filato, muna aiki a wannan gidan rediyo, a lokacin da nake wannan gidan rediyo na rika gabatar da shirye shiryen “Bayan Hakuri Sai Dadi,” da “Tsarabar kawaye” da sauransu.
Daga nan sai na je sashin talabijin na wannan gida, na rika gabatar da shirin “Duniyarmu ta Mata” da “Kiyaye Dokokin Hanya” da  wani shirin Ingilishi  mai suna “Women on the Mobe”  da  sauransu.
Ina nan a wannan gida na rediyo da talabijin na Jihar Filato sai aka sallame mu daga aiki a  shekarar  2001, cewa mu ba ’yan Jihar Filato ba ne. Ko kai Musulmi ne ko kai Kirista ne duk aka sallame mu daga aiki  A kan mu  ba ’yan asalin  Jihar Filato ba ne.
Tun kafin a sallame mu daga aiki a wannan gida, akwai wani shiri da nake gabatarwa tallar magin Royco mai suna “Mai dandanon Dadi”   wanda kamfanin Unileber suke daukar nauyi.
Wannan shiri ya shahara kwarai da gaske a arewacin kasar nan, a lokacin.  Domin a lokacin an rika gabatar da  shirin a gidajen rediyo da talabijin na nan Arewa. Kafin na samu wannan aiki na wannan shiri na tallar dandanon magin Royco na sha gwagwarmaya kwarai da gaske. Domin ni kadai ce macen da aka je aka gwada kan zan iya yin wannan shiri ko ba zan iya yi ba.
Bari in gaya maka  gaskiya na ji tsoro,  lokacin da aka zo za a  gwada ni. Domin wadanda aka zaba daga nan Arewa, aka ce mu je a gwada mu, sai na ga kamar duk sun fi ni. Ko daga wajen da nake aiki a lokacin, an samu ka-ce-na-ce kafin a amince  a tura ni. Amma da na je sai Allah Ya sa na kasance wadda aka zaba don gabatar da wannan shiri. Wannan shiri shi ne ya dada fito da ni a aikin jarida, kuma sai da na yi shekara 19 ina gabatar da shirin.
Da wannan shiri ya tsaya sai Allah Ya fito da wannan aiki na gidan rediyon Unity FM Jos. Wanda tsohon Ministan Watsa Labarai da Sadarwa Alhaji Ibrahim Dasuki Nakande ya bude. Dama shi  abokin maigidana ne, don haka sai ya yi wa mai gidana magana cewa yana son ya ba ni wannan aiki, na jagorancin wannan gidan rediyo. Amma Allah da ikonSa, kafin a bude wannan gidan rediyo Allah Ya yi wa maigidan nawa rasuwa. Maigidana ya ba ni goyon baya kwarai da gaske, kan wannan aiki na gidan rediyo. Ni ban san irin yadda zan kwatanta mijina ba, kan wannan aikin rediyo da nake yi. Domin ka san wasu mazaje ba sa son matansu su yi aikin jarida ko aikin asibiti, amma shi maigidana ba shi da wata damuwa kan wannan al’amari.
 A lokacin da aka bude wannan gidan rediyo a watan Mayu na shekarar 2013, ina ganin ba mu wuce mutum uku ko hudu ba. Amma a yanzu muna da ma’aikata sama da 20 a gidan rediyon.
Nasarorin da na samu:
 A gaskiya  na samu nasarori masu yawa a dukkan wuraren da na yi aiki. Domin a lokacin da nake aiki a gidan Rediyo da Talabijin na Jihar Filato, an ba ni lambar yabo kan wadda ta kware wajen shirye- shirye a gidan rediyon. Haka a bangaren talabijin ma na samu nasarori masu tarin yawa.  
Duk wani shiri za a ce a neme ni, nakan yi, domin babu abin da za ka yi, ka bata mini rai duk abin da aka ce in yi a aikin rediyo zan yi. Yaro karami sai ya koya mini aiki, domin wanda ya koya mini yadda ake gyara shirye-shirye a talabijin, yaro ne karami a wajena, kuma ban nuna girman kai ba.
Bayan haka na samu nasarori masu yawa a matsayina na jagorar wannan gidan rediyo na Unity FM Jos. Domin na samu kyaututtukan karramawa da dama tun daga lokacin da aka bude  gidan rediyo nzuwa wannan lokaci.  
Na samu lambobin yabo sama da 20 a wannan gidan rediyo, kan yadda muke gudanar da shirye-shiryenmu.
kalubalen da na fuskanta:
A gaskiya na fuskanci kalubale da dama kan wannan aiki. Domin a duk inda mace take aikin shugabanci,  mazan da suke wajen sukan dauka cewa yaya za a yi mace ta jagorance su. Don haka ina fuskantar kalubale kan wannan hali, amma ni ban  damu ba.  Domin ni ba raguwa ba ce, da   raguwa ce ni, da ban samu nasarorin da na samu ba.
Domin maza da yawa abin da nake yi gani suke yi ban iya ba. Ni kuma ina nuna musu cewa na iya, amma ta bangaren da ban iya ba, ba na yin girman kai, nakan tambaya.Domin ka ga kamar aikin kwanfuta ban iya ba a da, amma yara kanana ne suka koya mini. Wannan ba wani abin  kunya ba ne. Babu shakka na fuskanci kalubale da dama, amma sakamakon addu’a Allah Ya ba ni nasara.
Wane aiki ne kika so ki yi lokacin da kike karama?
Ni tun ina karama aikin jarida ne ya shige ni, domin a lokacin da nake karama a Kaduna akwai ’yan jarida irin su Khalifa Baba Ahmed da kasimu Yero ina kallonsu a talabijin. Wannan ya dada cusa mini kaunar aikin jarida tun ina karama.
Iyali:
Ina da ’ya’ya hudu maza uku da mace daya, kuma maigidana Allah Ya yi masa rasuwa.  Sai da muka shekara 37 da aure kafin Allah Ya yi masa rasuwa.
Tufafin da nafi so:
Na fi son dogayen riguna da tufafin mata  na mutunci.
Abincin da na fi so:
Na fi son cin tuwo da miyar ganye ko miyar yauki kuma ina son cin ’ya’yan itatuwa.
Abin da nake son a rika tunawa da ni:
Ina son a rika tunawa da ni a matsayin mace mai gaskiya da bin ka’ida da kuma iya aiki da kowane irin mutum.
Shawarata ga mata:
Shawara ta ga mata ita ce,  su tashi tsaye su nemi ilimi. Domin ilimi ba na maza ne kawai ba. Idan mace ta tashi ta yi ilimi babu inda ba za ta iya zama ta yi aiki ba. Kuma babu mutumin da ba za ta iya zama ta yi aiki da shi ba. Kuma mata su san yadda za su yi mu’amula da jama’a kuma su rika yin hakuri, domin hakuri shi ne ke gaba da komai.