Mata ku tashi ku rungumi harkokin siyasa – Afiniki benmak

Misis Afiniki benmak ita ce  shugabar mata ta jam’iyyar APC reshen Jihar Filato. A wannan tattaunawar da ta yi da wakilinmu, ta yi bayani kan irin kalubalen da ta fuskanta da kuma yanayin tafiyar  mata a harkokin siyasar Nijeriya. Tarihina:Ni sunana Misis Afiniki benmak.    An haife ni ne  a garin  Maiduguri a shekarar 1973, saboda […]

Mata ku tashi ku rungumi harkokin siyasa – Afiniki benmak
Mata ku tashi ku rungumi harkokin siyasa – Afiniki benmak

Misis Afiniki benmak ita ce  shugabar mata ta jam’iyyar APC reshen Jihar Filato. A wannan tattaunawar da ta yi da wakilinmu, ta yi bayani kan irin kalubalen da ta fuskanta da kuma yanayin tafiyar  mata a harkokin siyasar Nijeriya.

Tarihina:
Ni sunana Misis Afiniki benmak.    An haife ni ne  a garin  Maiduguri a shekarar 1973, saboda mahaifina soja  ne, a lokacin aiki ya kai shi can garin na Maiduguri. Amma ni  ’yar asalin karamar Hukumar Langtang ta Arewa ce dake Jihar Filato. Na fara makarantar firamare a garin Langtang, saboda  ban yi rayuwa da mahaifina ba. Na zauna da wata  ’yar uwar mahaifiyata ne a garin na Langtang.  Na yi makarantar firamare a nan bayan da na kammala na shiga makarantar sakandire, amma bayan na yi aji 5 sai na tsaya saboda rasuwar mahaifina.
Daga nan na shiga harkokin siyasa, tun daga mazabata na shiga jam’iyyar PDP daga nan na shiga jam’iyyar AD daga nan na shiga jam’iyyar Labour daga nan kuma na shiga jam’iyyar APC, wadda a yanzu nake shugabancin bangaren mata na wannan jam’iyya  a nan Jihar Filato. Abin da ya karfafa mini gwiwar shiga siyasa. Abin da ya sa na shiga harkokin siyasa shi ne don na lura siyasa tana da kyau, domin mutum zai samu damar taimaka wa al’umma  ta hanyoyi da dama.  

Dalilan da suka sanya aka zabe ni:
Babban dalilin da ya sanya aka zabe ni shugabar mata ta jam’iyyar APC a  Filato shi ne, saboda ganin cewa na cancanta kuma a rayuwata duk abin da na sanya a gaba, ina yi ne da zuciya daya. Don haka nake ganin ya sanya aka zabe ni, a kan wannan kujera.

kalubalen da na fuskanta:
A matsayina na mace na fuskanci kalubale da dama  musamman a harkokin siyasa, domin siyasa duk da cewa tana da dadi, amma siyasa wata aba ce mai wahala. Akwai wadanda suka nuna suna so na, akwai kuma wadanda suka nuna ba sa sona saboda suna ganin cewa ba ni da karatu mai zurfi. Sun manta cewa siyasa ba maganar karatu ba ne. Shi iya tafiyar da jama’a  ko kuma jagorancin jama’a baiwa ce daga Allah domin za ka ga wani yana da karatu mai zurfi, amma Allah bai ba shi baiwar iya tafiyar da jagorancin jama’a ba. Amma sai ka ga wani ba shi da karatu mai zurfi amma Allah ya yi masa baiwa da basira na iya tafiyar da jagorancin jama’a. Don haka ina yi wa Allah godiya kan wannan baiwa da Ya ba ni na iya tafiyar da jagorancin jama’a.

Abin da na so yi lokacin da nake karama:
A lokacin da nake karama na taso da burin in yi karatu domin in zama malamar asibiti, amma sai Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa. Rasuwar mahaifina sai ta katse mini wannan buri nawa, nan take na bar makaranta na yi aure.

Mata a harkokin siyasa a Nijeriya:
Tafiyar mata a harkokin siyasar Nijeriya babu shakka akwai cigaba a halin yanzu, idan muka kwatanta da shekarun baya.  Domin a  yanzu akwai mata a majalisar dattawa da wakilai ta tarayya  da majalisun jihohi, sannan kuma ga ministoci mata da shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada. Kuma ga mata kwamishinoni da  gwamnonin jihohin  kasar nan suka nada. Amma duk da haka  ina rokon mata, kan su tashi su rungumi harkokin siyasa domin su samu damar taimaka al’umma.

Iyali:
Na yi  aure a shekarar 1992  kuma na haifi yara guda 7 amma yanzu guda 4 ne suke raye kuma dukkansu mata ne.

Abincin da na fi so:
Na fi son tuwo da miyar ganye sannan ina son wake.

Tufafin da na fi so:
 Tufar da na fi so ita ce doguwar riga.

Abin da nake son a rika tunawa da ni:
Ina son mutane su rika tunawa da ni a matasayin wadda ta yi abubuwan da suka  taimaka wa mata a Jihar Filato da kuma Najeriya baki daya.

Shawara ga mata:
Shawarata ga mata ita ce su tashi su rungumi harkokin siyasa. Kuma ina kira ga gwamnatocin kasar nan kan su kara bai wa mata dama a harkokin siyasar kasar nan.