Mata magoya bayan PDP dubu 10 sun koma APC a Jihar Kebbi
Kimanin mata magoya bayan Jam’iyyar PDP dubu 10 ne suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi a wannan mako. Shugaban mata ta PDP ta karamar Hukumar Dandi-Kamba, Hajiya Sahura ’Yarkura Dolakaina ce ta jagoranci dimbin matan da suka fito daga kananan hukumomin jihar 21 zuwa APC.A wani gaggarumin taro da aka yi a […]
Kimanin mata magoya bayan Jam’iyyar PDP dubu 10 ne suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi a wannan mako.
Shugaban mata ta PDP ta karamar Hukumar Dandi-Kamba, Hajiya Sahura ’Yarkura Dolakaina ce ta jagoranci dimbin matan da suka fito daga kananan hukumomin jihar 21 zuwa APC.
A wani gaggarumin taro da aka yi a ofishin Jam’iyyar APC, jiga-jigan matan PDP da suka rufa mata baya sun hada da Hajiya Halima Dolakaina da Hajiya Lubabatu da Hajiya Halimatu da magoya bayansu daga kananan hukumomin jihar.
Da take bayani a wurin karbarsu, shugabar mata ta Jam’iyyar APC ta Jihar Kebbi, Hajiya Tsahara Bawa ta ce ta rasa abin da za ta ce saboda murna, domin gaskiya ta yi halinta.
Shugabar matan ta ce su da suka dade a cikin APC da wadanda suka shigo ta a ranar sun zama daya, kuma da yarda Allah za a yi musu adalci.
Hajiya Tsahara Bawa ta shaida masu cewa Jam’iyyar APC ba jam’iyyar masu nadi ba ne jam’iyya ce mai bin ka’idoji da doka da oda, kowane mukami za a zabe shi ne kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Da take maida jawabi a madadin wadanda suka sauya shekar Hajiya Sahura ’Yarkura Dolakaina, ta ce dalilin barinsu PDP zuwa APC shi ne yanzu PDP a Jihar Kebbi ta zama fanko, ba komai a cikinta, sai kashe ’ya’yanta da take yi, shi ya sa kafin ta kai gare su suka yanke shawarar su gudu su bar ta.
Hajiya Sahura ta ce shekara 16 suna cikin PDP amma ba ta tsinana wa talakawan Jihar Kebbi komai ba, daga talauci da kuncin rayuwa sai rarrabuwar kai da kashe dukiyar jama’a da kama -karya.
Da yake jawabi shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Barista Attahiru Maccido, ya ce Jam’iyyar PDP a jihar ciwon Ebola ya kamata sakamakon yadda dubban jama’a daga ko’ina a cikin jihar suke sauya sheka zuwa APC, saboda yadda PDP da ’yan kanzaginta suka kware wajen kama-karya, “to daga shekarar 2015 badakalar ta zo karshe da yardar Allah,” inji shi.
Ya yi kira ga al’ummar jihar su kara hakuri zuwa zaben badi, inda za su ga canji a kan irin matsalolin da suke damunsu idan Jam’iyyar APC ta kafa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kebbi.