Mata masu kunar bakin wake: Cikin hayyacinsu suke ko kuwa batar musu da hankali ake?
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban […]
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Suna cikin hayyacinsu – Muhammad Ibrahim
Malam Muhammadu Ibrahim Adamu: “Ni ina ganin ba sai an yi wani dogon sharhi ba dangane da aika-aikar wadannan ’yan matan masu tayar da bama-bamai. Dalilina kuwa na farko, tsakanin sojoji da ’yan Boko Haram Allah kadai ya san iya adadin mutanen da suka kashe tun alokacin da aka shiga rikicin a kasar nan, don haka idan aka yi la’akari da wannan ba abin mamaki ba ne a samu a cikin wadannan mutanen da suka kashe din akwai iyayen irin wadannan ’yan matan da wasu ’yan uwansu a ciki; su ne abin ya kai musu suka gwammace su ma gara su mutu.
“Sai kuma abu na biyu, akwai wasu mutanen wadanda ita gwamnatin kasa take zargin su din nan ’yan Boko Haram ne, ta sa aka kame su aka garkame a gidajen yari ba tare da an yanke masu hukunci ba, don haka batun ko a ce wadannan ’yan matan wai suna cikin rikicewar hankali ba ta taso ba, kawai sai dai a ce bakin ciki ma yana iya sanya wasu su aikata muguwar barna da za ta jefa rayuwar jama’a a cikin barazana.”