Mata masu kunar bakin wake: Cikin hayyacinsu suke ko kuwa batar musu da hankali ake? 1

A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban […]

Mata masu kunar bakin wake: Cikin hayyacinsu suke ko kuwa batar musu da hankali ake? 1
Mata masu kunar bakin wake: Cikin hayyacinsu suke ko kuwa batar musu da hankali ake? 1

A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Ba na zaton suna cikin hayyacinsu – Yusuf Usman

Yusuf Usman: “Ni dai a tawa fahimtar, ba na tunanin cewa mutumin da yake cikin hankalinsa zai saka bam a jikinsa ko wani ya saka masa sannan ya san tabbas zai mutu ya rabu da duniya, amma ya je ya kai hari ko ya tayar da bam din. Idan kuwa har wadannan ’yan matan da hankalinsu suke yin wannan abu, to kuwa akwai wata yaudara da ake yi musu a tafiyar da tunaninsu. Bayan haka kuma ina ganin za a iya gusar musu da hankali ko dai a ba su kayan maye su sha su bugu, kafin a aika su wajen kai harin, ko kuma ta kawar da hankalinsu ta hanyar tsubbace-tsubbace. Duk wadannan kuwa masu yiwuwa ne. Amma kuma a game da cewa ko daga ina wadannan ’yan mata suka fito, to wannan ba zan iya cewa komai ba a nan, don ya wuce iyakar tunanina.”