Mata masu kunar bakin wake: Cikin hayyacinsu suke ko kuwa batar musu da hankali ake? 2
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban […]
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Ana juyar da hankulansu ne – Malam Kabiru
Malam Kabiru Muhammad Chidawa: “A iyaka fahimta ta dangane da wannan al’amari na kai hare-haren bama-bamai da kananan yara ’yan mata suke yi a kasar nan. A gaskiya ba a cikin hankalinsu suke kai irin wadannan hare-hare ba. Domin a kasar nan kamar a kauyukanmu, akan sami kananan yara wadanda jahilci ya yi masu yawa. Za a iya ba irin wadannan yara wani abu a ce su kai wani wuri, su karba su kai ba tare da wani tunani ba. Haka kuma za a iya yin amfani da tsatsuba a juya kwakwalensu, wajen tura su su kai irin wadannan hare-haren bama-bamai. Amma ba na tunanin akwai wanda yake cikin hankalinsa da zai iya kai irin wadannan hare-hare da zai hallaka kansa, ya kuma hallaka sauran jama’a ba, ba tare da an juya masa hankalinsa ba. Don haka irin wadannan kananan yara a ganina ana ba su kayan maye ne ko kuma ana amfani da tsatsuba ne wajen juyar masa da hankali kafin su kai irin wadannan hare-hare. Ko kuma ana amfani da jahilcinsu ne a tura su kai irin wadannan hare-hare.”