Mata masu kunar bakin wake: Cikin hayyacinsu suke ko kuwa batar musu da hankali ake? 3
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban […]
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Ba a cikin hayyacinsu suke ba – Salisu Ibrahim
Alhaji Salisu Ibrahim: ‘’Duk wanda ya tsaya ya yi tunani zai fahimci cewa wadannan kananan yara mata da ake turawa su kai irin wadannan hare-haren bama-bamai ba a cikin hayyacinsu suke kai irin wadannan hare-hare ba. Domin idan da a cikin hayyacinsu suke kai irin wadannan Hare-hare, ba za su yi ba don babu wanda yake cikin hayyacinsa da zai je ya hallaka kansa da kansa. Bayan haka ina tunanin wadannan yara irin ’yan matan ne da aka sace a Chibok ne aka juya kwakwalwarsu ake amfani da su wajen kai irin wadannan hare-haren bama-bamai. Amma a tunina babu wani mutum mai hankali da zai je ya hallaka kansa da kansa. Duk mutumin da zai je ya dauki bam ya je ya kashe kansa tare da sauran jama’a ba za a iya daukarsa a matsayin mai hankali ba.”