Mata masu kunar bakin wake: Cikin hayyacinsu suke ko kuwa batar musu da hankali ake? 4
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban […]
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Komai na iya faruwa da matan – Musa Umar
Musa Umar Yakasai: “A nawa ra’ayin, ba wai lallai ne sai an kawar da hankalin ’yan matan da suke kai harin bam ba, domin akwai hanyoyi daban-daban. Na farko ma dai ta iya yiwuwa su kansu ba su san bam aka saka musu a jikinsu ba, an dai tura su ne su je wajen, amma kuma mai tayar da bam din yana nan a gefe a makale, suna zuwa inda ake so, sai kawai ya tayar da shi da na’ura. Wani abin kuma shi ne, halin kunci da tsananin rayuwa da ake ciki a Najeriya, da akwai nau’in mutanen da suke jin rayuwar ma ta ishe su. Idan ’yan Boko Haram suka kama irin wadannan mutanen za su iya amfani da su a cikin sauki, tun da wasu da dama suna ganin ko dai gwamnati ko ma’ikatan tsaro masu damara sun takura musu, don haka babu komai a tsakaninsu sai gaba. A kan haka za a iya amfani da irin wadanda ba su da uwa ko uba, su rika kai irin wannan harin.”