Mata masu kunar bakin wake: Cikin hayyacinsu suke ko kuwa batar musu da hankali ake? 5
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban […]
A ’yan kwanakin nan, an samu bayyanar wasu mata da ke kunar bakin wake, suna fasa bama-bamai da sunan Boko Haram. Ana ta mamakin yadda al’amarin ya kasance haka har ma ake tunanin shin da amincewarsu ne suke wannan ta’addanci ko kuwa ana batar musu da hankali ne tukunna? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Ba cikin hayyacinsu suke ba – Adamu Muhammad
Malam Adamu Muhammed “Ni a fahimta ta, akwai alamar wadannan ’yan matan ba a cikin hayyacinsu suke aikata irin wannan barnar ba. Dalilina kuwa shi ne, duk wanda yake a cikin hankalinsa ba zai taba yarda da ya mika rayuwarsa ga hallaka ba. Don haka wadannan ’yan matan ina ganin mai yiwuwa a ce irin wadannan ’yan matan da ’yan Boko Haram suke sacewa su kai su boye da su domin biyan miyagun bukatunsu, a ciki suka ba su irin wannan horon na sabon salo tare da tilasta musu su sha wasu ababen maye da zai rakitar masu da kwakwalwarsu, kafin daga nan sai su daura masu wadannan bamabaman, sannan sai su tura su wuraren da suke bukata, su shiga su hallaka kawunansu da sauran mutane kamar yadda muke ganin yake faruwa a yau a cikin kasar nan. Don haka sai dai mu ce Allah Ya kyauta.”