Mata masu safarar yara sun shiga hannu a Legas
Jami’an ’yan sanda sun yi nasarar kame wasu mata da suka yi safarar yara kanana su 26 daga Jihar Kano a daidai lokacin da suke yunkurin shiga da su Legas.A cewar Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Abdulmajid Ali, lokacin da yake gabatar da matan su uku da yaran da aka yi dauko su, ’yan mata […]
Jami’an ’yan sanda sun yi nasarar kame wasu mata da suka yi safarar yara kanana su 26 daga Jihar Kano a daidai lokacin da suke yunkurin shiga da su Legas.
A cewar Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Abdulmajid Ali, lokacin da yake gabatar da matan su uku da yaran da aka yi dauko su, ’yan mata 25 da namiji daya, wadanda ba su wuce shekara 8 zuwa 10 ba, rundunar ’yan sanda ta cafke su ne a tashar mota da ke garin Ogere a Jihar Ogun, bayan da aka ankarar da su cewa an ga wasu mata masu safarar yara; inda nan take ya ba da umarnin a kame su.
Matan da ake zargi da safarar yaran su ne Zainab Ahmad ’yar shekara 18 da A’isha Abdullahi mai shekara 55, sai Zulaihat Abdulmalik mai shekara 45.
Wadanda ake zargin sun shaida wa Aminiya cewa sun yiwo safarar yaran ne domin zuwa da su Legas su sama musu aikace-aikace irin na su wanke-wanke da sayar da abinci da yi wa makafi jagora. Tuni dai rundunar ’yan sandan ta mika su ga hukumar kare hakkokin yara bayan ta kammala bincikenta.
Iren-iren wadannan yara akasari ’yan mata su ne za ka yi ta cin karo da su a manyan hanyoyin cikin garin Legas da Ibadan suna barace-barace, a daidai lokacin da takwarorinsu Yarabawa ke a makarantu suna neman ilimi don ingantuwar rayuwarsu.