Mata-maza jinsi ne na uku a rukunin al’umma – Hukuncin Kotun kolin Indiya

Kotun koli ta kasar Indiya ta yanke hukunci kan mata-maza, inda ta ba su matsayin “jinsi na uku,” kamar yadda jaridar ‘Times of India’ ta bayyana. Wannan kuwa ya biyo bayan karar da aka gabatar a gabanta, don tantance kimar jinsin mata-maza a harkokin zamantakewa da tattalin arziki a kasar, al’amarin da ake ganin ya […]

Mata-maza jinsi ne na uku a rukunin al’umma – Hukuncin Kotun kolin Indiya

Wani yanayi na mata-maza a kasar IndiyaKotun koli ta kasar Indiya ta yanke hukunci kan mata-maza, inda ta ba su matsayin “jinsi na uku,” kamar yadda jaridar ‘Times of India’ ta bayyana. Wannan kuwa ya biyo bayan karar da aka gabatar a gabanta, don tantance kimar jinsin mata-maza a harkokin zamantakewa da tattalin arziki a kasar, al’amarin da ake ganin ya mayar da irin wannan jinsi na mutane koma-baya.
Sabanin da ake da jinsi biyu na mace da namiji, kotun Indiya ta martaba mata-maza, inda ta ba su kimar “jinsi na uku,” ne a rukunin al’umma, kamar yadda ta yanke a hukuncinta. Sannan kotun ta bayar da umarni ga jihohi kan dole su samar da makewayi da sassan ayyuka da wuraren kula da lafiya na musamman, don biyan bukatun jinsi na uku. Ta kuma bayar da umarni ga hukumomin kula da juin dadi da walwalar al’umma, kan su rika fadakarwa kan muhimmancin wannan jinsi, ta yadda zz a daina kyararsu. Har ila yau, a cikin hukuncin kotun kolin an yi kari da cewa idan mutum a kashin kansa ya bukaci a yi masa aikin fida (tiyata), don sauya jinsinsa zuwa namiji ko mace, ba za a nuna masa/mata wariya ba.
Kotun kolin ta bayyana cewa mata-maza na da ’yancin samun shiga makarantun ilimi, ko neman aiki a matsayin jinsi mai kima ta uku. Don haka yanzu a kasar Indiya ake yi musu lakabi da “hijiras,” wkto asbin da a Turancin Ingilishi ake kira “Transgender.” Kotun dai ta tabbatar musu da ’yancin samun ilimi da kuma bayar da aiki. Wannan kuma shi ne karo na farko da jinsin na uku ya samu amincewa a harkokin kasar.
A da ana baiwa mata-maza kimar darajarsu a kasar Indiya, amma daga bisani al’amura suka sauya, har ta kai ga ana nuna musu wariya, ana cin zarafinsu. “Don haka kotun ta yi amfani da sashen doka  na 377 na IPC, sashen da ta ce ‘yan sanda da sauran hukumomi na mummunan amfani da shi don keta haddin wannan rukuni na mutane, a harkokibn zamantakewa da tattalin arziki,” a cewar sanar da kotun koli ta bayar.
Shugaban kungiyar fafutikar hakkin mata-maza, Lakshmi Narayan Tripathi, ya ce “wannan ci gaba da aka samu a kasar ya dogara ne kacokan wajen tabbatar da hakkin dan Adam, don haka muna farin ciki da wannan hukunci da koun koli ta janye, al’amarin da ya tabbatar mana da hakkokinmu.”

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu