Mata-maza na iya amfani da bandakin mata – Kotun Colarado

Wata kotu a Jihar  Colarado ta Amurka ta yanke hukunci kan cewa maza-matan yaro da aka haifa, wanda yake ganin kansa a matsayin mace, zai iya amfani da bandakin mata a makarantar elemantare, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.Iyayen yaron ne suka kai kara, bayan da Jami’an Hukumar Makarantar Eagleside Elementry ta […]

Mata-maza na iya amfani da bandakin mata – Kotun Colarado
Mata-maza na iya amfani da bandakin mata – Kotun Colarado

Wata kotu a Jihar  Colarado ta Amurka ta yanke hukunci kan cewa maza-matan yaro da aka haifa, wanda yake ganin kansa a matsayin mace, zai iya amfani da bandakin mata a makarantar elemantare, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.
Iyayen yaron ne suka kai kara, bayan da Jami’an Hukumar Makarantar Eagleside Elementry ta umarci yaron ya rika amfani da wurin hutawar malamai ko ofishin nas, amma ban da wurin wankan mata. Iyayen wannan yaro mai suna Coy Mathis sun fahimci ana nuna wa dansu kyara, don haka suka shiga fafutika kwato hakkin yaron a Hukumar Fafutikar Hakkin al’umma da ke Colarado.
Kathryn Mathis, mahaifiyar yaron ta bayyana cewa “za ta samu makoma mai kyau, in aka kawo karshen wannan takaddama, domin ba abin kunya ba ne.”
Mat Staber Lauya mai fafutikar hakkin al’umma, ya bayyana cewa, matsalar maza-mata, al’amari na cin fuska ga masu fafutikar hakkokin al’umma, matukar ba a kawo karshen al’amarin ba.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda