Mata miliyan 15 ke zubar da ciki a Indiya duk shekara
Wata cibiyar bincike mai suna Guttmacher Institute’s research da ke New York, ta gano cewa ana zubar da ciki miliyan 15 a kasar Indiya duk shekara. Amma sai dai wannan kididdigar ta Guttmacher Institute’s research, ta dara wadda hukomomi a kasar ta Indiya suka bayar kamar yadda BBC ta ruwaito. Hakanan kuma cibiyar binciken ta […]

Wata cibiyar bincike mai suna Guttmacher Institute’s research da ke New York, ta gano cewa ana zubar da ciki miliyan 15 a kasar Indiya duk shekara.
Amma sai dai wannan kididdigar ta Guttmacher Institute’s research, ta dara wadda hukomomi a kasar ta Indiya suka bayar kamar yadda BBC ta ruwaito.
Hakanan kuma cibiyar binciken ta gano cewa mafi yawan matan Indiyan da suke zubar da cikin, suna amfani ne da kwayoyi ba tare da bin ka’ida ba a gidajensu, kuma ba tare da tuntubar yadda za a yi amfani da su ba.
Gwamnatin kasar ta Indiy, ta ce ana zubar da ciki kasa da dubu 700 ne a kowace shekara a kasar ne a nata kididdigar.
Ita dai gwamnatin ta samo nata adadin ne bayan ta hada bayanai daga asibitocin jihohi da kuma dakunan maganin sha ka tafi.
Sannan kuma masu binciken sun ce matan kan sha wuya a yayin zubar da cikin.