Mata na da gudunmawar da za su bayar a harkokin siyasa – Sakatariya
Hajiya Hauwa Ahmed, ita ce Sakatariyar karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, kuma ita ce kadai mace mai rike da wannan mukami a jihar. A tattaunawarta da Aminiya ta ce mata za su ci gaba da ba da gudunmawa a fagen siyasar kasar nan kamar yadda ake gani a wannan lokaci: Aminiya: Me ya ba […]
Hajiya Hauwa Ahmed, ita ce Sakatariyar karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, kuma ita ce kadai mace mai rike da wannan mukami a jihar. A tattaunawarta da Aminiya ta ce mata za su ci gaba da ba da gudunmawa a fagen siyasar kasar nan kamar yadda ake gani a wannan lokaci:
Aminiya: Me ya ba ki sha’awar shiga cikin harkokin siyasa duk da cewa ke matar aure ce?
Hauwa Ahmed: Na fara sha’awar siyasa ne saboda maigidana dan siyasa ne. Shi ne ma yake sanya ni in taimaka masa a fannin mata abokan siyasarsa daga nan ne na samu kwarewa sosai cikin siyasa da mu’amala da al’umma.Na fara siyasa ne a 1999 da Jam’iyyar PDP lokacin da aka dora kasar nan bisa tsarin dimokuradiyya, sai dai ban taba rike kowane mukami ba kuma ban taba tsayawa takara ba koda ta shugabancin jam’iyya ba.
Amma akwai wasu kungiyoyi na mata da nake jagoranta wadanda ba su da nasaba da harkokin siyasa, wadanda suka yi fice wajen taimaka wa mata a fannoni da yawa, akwai wata kungiya a Unguwar Darmanawa da wata a karamar Hukumar Bunkure. Ta siyasa ita ce wadda muka kafa mai suna kungiyar ci gaban Jam’iyyar APC, ko shakka babu wannan kungiya ta yi aiki sosai wajen samun nasarar jam’iyyar a karamar Hukumar Tarauni.
Aminiya: Wane kalubale kika fuskanta a gwagwarmayar da kika yi?
Hauwa Ahmed: To, duk dan Adam ba ya rasa wani kalubale a rayuwa da ya fuskanta, ina kara godiya ga Allah cewa ban hadu da kalubale mai wahalar warwarewa ba a rayuwata. Kusan duk wani abu mawuyaci da ya same ni, Allah cikin ikonSa Yana ba ni damar warware shi, domin kamar yadda na bayyana maka maigidana dan siyasa ne, saboda haka gaskiya babu wani babban kalubale da yake mai nauyi a gare ni bisa taimakon Allah.
Aminiya: Me za ki ce dangane da gudummawar mata a harkokin siyasar kasar nan musamman yanzu da Najeriya ta zauna kan tsarin dimokuradiyya?
Hauwa Ahmed: Yana da kyau a fahimci cewa shigar mata cikin harkokin siyasa abu ne mai matukar alheri, saboda mace ai uwa ce ga al’umma. Sannan idan aka waiwayi tarihi, mata sun yi kokari sosai wajen rike mukamai ko jagoranci a duniya. Don haka duk inda mata suka rike ana samun amana da kwazo a wurin, domin mata suna da matukar kokari a duk inda suka samu kansu. Duk da cewa ana ganin shigar mata cikin harkokin siyasa abu ne da yake da matsala, amma idan mace ta kasance bisa tsari na gaskiya da kame kai, ko shakka babu za ta ba da gagarumar gudunmawa a duk inda ta samu kanta. Kuma ina tabbatar da cewa mata za su ci gaba da ba da gudunmawarsu a sha’anin siyasar kasar nan ta yadda za a samu kasa mai albarka cikin yardar Allah.
Ina fata ’yan siyasa za su kara ba mata damar don ba da tasu gudunmawar da za su taimaki al’umma.
Aminiya: Yaya kika dauki wannan aiki na Sakatariyar karamar Hukuma a matsayinki ta mace?
Hauwa Ahmed: Na dauki wannan aiki a matsayin bauta wa karamar Hukumar Tarauni da Jihar Kano da kuma kasata. Babu shakka ina farin ciki ganin cewa ina da wata dama ta bada gudunmawata ga al’umma. Kuma ina fata Allah Ya kara mana juriya da dauriyar gabatar da ayyukan alheri ga al’umma kamar yadda tsohon Gwamna Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da sabon Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da kuma Shugaban karamar Hukumar Tarauni Injiniya Muktar Umar Yarima suke yi, wanda shi ne ya ga dacewata ya ba ni matsayin Sakatariyar karamar hukumarsa.
Aminiya: Ko akwai wani abu da karamar hukumarku ta yi wanda ya yi miki dadi bisa taimakawarki?
Hauwa Ahmed: Akwai shirin kyautata rayuwar matasan da suke shaye-shaye da karamar hukuma ke yi. Wannan shiri gaskiya yana yi wa duk iyaye mata dadi, domin ’ya’yansu ne suke amfana da wannan shiri. Kuma karamar hukuma tana kokari sosai wajen inganta rayuwar al’umma kamar yadda ake bukata. Ina fata dukkan matakan gwamnati uku da muke da su wato tarayya da jihohi da kananan hukumomi za su bullo da shirye-shiryen kyautata halayyar matasa domin su ne kashin bayan kowace kasa. Haka zai yi kyau Gwamnatin Tarayya da na jihohi su kara yawan mata a cikin harkokinsu domin na tabbata za a cimma gagarumar nasara idan aka kara ba mata dama a gwamnati. Sannan yana da kyau a inganta ofishin matar Shugaban kasa domin mata za su kara samun dama wajen taimaka wa ’yan uwansu mata musamman ma a yankunan karkara da kuma birane, domin su mata suna da wata kwarewa kan gano matsalolin ’yan uwansu mata da yara kanana.