Mata na da rawar takawa a siyasa – Hafsat Ganduje
Uwargidan Gwamnan Jihar Kano Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta nanata bukatar mata su fito a dama da su a al’amuran siyasa a kasar nan. Hajiya Hafsat Ganduje ta bayyana a haka a wajen taron koli kan shugabanci da wata kungiyar bunkasa dimokuradiyya mai suna Democractic Action Group (DAG) da hadin gwiwar Hukumar Raya kasashe […]
Uwargidan Gwamnan Jihar Kano Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta nanata bukatar mata su fito a dama da su a al’amuran siyasa a kasar nan. Hajiya Hafsat Ganduje ta bayyana a haka a wajen taron koli kan shugabanci da wata kungiyar bunkasa dimokuradiyya mai suna Democractic Action Group (DAG) da hadin gwiwar Hukumar Raya kasashe ta Birtaniya (DFID), suka shirya.
Uwargidan Gwamnan ta ce mata na da rawar takawa a bangarori da dama na rayuwa ciki har da shugabancin al’umma matukar suna samu cikakken ilimi. “Mata suna da sauki wajen abin da ya shafi cin hanci da rashawa kuma a matsayinsu na iyaye masu bayar da tarbiyya za su tsaya wajen ganin an samu nagartacciyar al’umma ta hanyar kayakkyawan shugabanci,” inji ta.
Hajiya Hafsat Ganduje ta yi kira ga matan su jajirce wajen neman ilimi, domin sai da ilimi kowane abu na rayuwa ke samuwa.
A jawabin Shugaban kungiyar DAG, Muhammad Mustapha Yahaya ya ce manufar taron shi ne a karfafa wa mata su shiga a dama da su a harkokin siyasa da shugabanci. “Binciken da muka gudanar a baya kan shugabancin mata a Jihar Kano mun gano gaba dayan jihar babu mata da ke rike da mukaman zababbun shugabanni, ko kansila mace babu a fadin jihar balle shugaban karamar hukuma ko ’yar majalisa,” inji shi. Ya ce rashin samun mata a siyasa ya jawo namiji ne Shugaban Kwamitin Mata a Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Mata da dama da suka halarci taron sun yi korafin cewa a lokuta da dama sukan yi yunkurin fitowa takarar sai dai maza ke tade musu kafafuwa tun daga zaben share-fage.