Mata na fargabar ‘mutanen boyen’ da ke datse musu gashi
Matan da ke yankunan Rajastan da Haryan a kasar Indiya na zaman fargabar mutanen boyen da ke datse musu gashi, inda a kalla mata 36 aka yi wa wannan ta’adi a yankin Mewat, baya ga wasu uku irin wadannan da aka ruwaito daga Yammacin birnin Delhi, wato kimanin mata 50 ke nan, kamar yadda […]
Matan da ke yankunan Rajastan da Haryan a kasar Indiya na zaman fargabar mutanen boyen da ke datse musu gashi, inda a kalla mata 36 aka yi wa wannan ta’adi a yankin Mewat, baya ga wasu uku irin wadannan da aka ruwaito daga Yammacin birnin Delhi, wato kimanin mata 50 ke nan, kamar yadda ’yan sanda suka sanar a Litinin din da ta gabata.
’Yan sanda sun ce a karkaswhin dokar hana bazuwar makamai aka yi rajistar wamnnan korafi na dates gashin mata, kamar yadda wasu suka kawo kara a daren Lahadin da ta gabata, wadanda suka fito daga kwauyen Kan gan Heri da ke Yammacin Chhawala ta Delhi.
“Mun samu koke daga mata uku da wani da ba su sani ba ya datse musu gashi. An a zargin wani gungun masu aikata miyagunh laifuka ked a alhakin wannan aika-aikar, musamman ma jin cewa mazauna yankuna sun koka kan fashi da makami. Muna zargin wasu matasa uku da hoton su ya bayyana a na’urar kyamarar tattara bayanai,” a cewar Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda Surender Kumar.
daya daga cikin m atan, Munish cewa ta yi, a lokacin da ta kusa isa gida bayan ta dawo daga kasuwa wajen karfe bakwai na yamma sai ta rika jin juwa, har ta fita hayyacinta. Lokacin da ta dawo cikin hayyacinta sai gane cewa an daddatse mata gashin kai.
“Abin mamakin ma shi ne, ‘yarta ’yar shekara shiuda da ke yi mata rakiya ba ta ga kowa ba,” a cewar jami’in.
Kuma matan da suka hada da Sri Debi and Omwati sun kawo rahoton irin wannan aikata-aika daga garuruwan da Omwati da ke kauyen Kangan ranar Lahadin makon jiya.
“Mutanen kauye na zaman dar-dar kan wannan farmaki da ake kai musu, kuma maza na sintiri cikin dare don kama masu laifi, amma mata na tsoron fita,” kamar yadda wani mazaunin kauyen Rambeer Shokeen ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na IANS.
Mafi yawan mazaunan kauyuka na ganin cewa wani ke yin tsafi ko masu tsatsuba ke da alhakin wannan farmaki, a cewar Shokeen.