Mata na shan tsangwama a Barno saboda binciken kwakwaf
A sakamakon rashin tsaron da Jihar Borno ke fuskanta, musamman ma yawan kai hare-haren kunar bakin wake da aka ce mata na kai wa kasuwanni ko wuraren taron jama’a, a yanzu mata na fuskantar tsangwama sakamakon binciken kwakwaf da ake yi musu.Wadansu daga cikin matan sun ce sukan shiga tashin hankali a duk lokacin da […]
A sakamakon rashin tsaron da Jihar Borno ke fuskanta, musamman ma yawan kai hare-haren kunar bakin wake da aka ce mata na kai wa kasuwanni ko wuraren taron jama’a, a yanzu mata na fuskantar tsangwama sakamakon binciken kwakwaf da ake yi musu.
Wadansu daga cikin matan sun ce sukan shiga tashin hankali a duk lokacin da suka fito daga gidajensu za su je unguwanni ko kasuwa, inda suke fuskantar tsangwama daga jami’an tsaro da ’yan kato da gora wadanda ake kira bibilian JTF.
Hajiya Falmata Muhammad, tana daya daga cikin wadanda suka fuskanci tsangwama sakamakon binciken kwakwaf, inda ta bayyana rashin jin dadinta.
“A gaskiya ban ji dadin yadda wata ’yar uwata mace ta yi mini a lokacin da zan shiga Kasuwar Monday Market ba, ta yi mini hakan ne da sunan bincike. Ta bincike ni tun daga kaina har zuwa kafata, sannan duk abin da nake dauke da shi ko sanye da shi, sai da ta warware mini shi. Daga nan ta rika fada mini wasu bakaken maganganu kamar ta kama ni da bam a jikina ne, kuma na tabbata na haife ta.” Inji Falmata.
Ta kara da cewa: “Ta ce mini wai kwadayin kudinmu mu iyayensu ya yi yawa, shi ya sa wannan abin ke faruwa, saboda haka ko ke wace ce zan duba ki, kuma in bincike ki babu abin da za ki iya yi.’’
Wata matashiya mai suna Yagana Bukar cewa ta yi “Yan gora sun sa na cire hijabina gaba daya, kuma sun zazzage mini jakata a lokacin da na hau Keke Napepe bayan mun isa shatale-talen Post Office, duk da cewar ’yar uwata ce mace, amma ban ji dadi ba, kowane irin bincike ake yi ai ya kamata a ce akwai mutunci da girmamawa.”
Ta ce abin da ya fi ba ta haushi shi ne ba a binciken maza, akan bar su su wuce, wannan bai dace ba. “ai maza su suka fara kawo maganar harin kunar bakin wake da bama-bamai a Borno, amma me ya sa ba za a bincike su ba sai mu mata? A matan ba duka ba ne suka taru suka zama daya, ya kamata a duba wannan al’amari.’’
Misis Mary Bwala, ita ma ta samu kanta a cikin wannan matsalar binciken.
Ta ce “Binciken yana da kyau amma a wani lokaci yakan wuce gona da iri, don masu binciken suna bincike inda bai kamata su bincika ba, kuma suna fada wa mutane wasu maganganu wadanda ba su dace ba.”
Wakilinmu ya tuntubi daya daga cikin jagororin ’yan kato da gora (bibilian JTF), mai suna Modu Bukar, inda ya ce za su yi bincike a kan al’amarin.
“To ai mata ne ke duba mata, mu a wurinmu bai dace maza su duba mata ba, mun tsara mata ne za su duba mata ’yan uwansu, a yayin da maza za su duba maza, kuma zargin musgunawa ni ban sani ba, idan ma akwai to za mu bincika, kuma mu ja musu kunne, amma a iya sanina jami’an tsaro sun koyar da mu yadda za mu yi mu’amala da mutane.”