Mata su ne ginshikin al’umma
TarihinaAn haife ni a shekara ta 1966 kuma a karamar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano. Na fara karatun Islamiyya a wajen Malam Muhammad sannan na yi karatun firamare a firamaren Gandun Albasa a shekarar 1972 kafin daga bisani na kammala a firamaren Bagauda dake Kano. Na yi karatun sakandare a makarantar ‘yammata ta Shekara inda […]
Tarihina
An haife ni a shekara ta 1966 kuma a karamar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano. Na fara karatun Islamiyya a wajen Malam Muhammad sannan na yi karatun firamare a firamaren Gandun Albasa a shekarar 1972 kafin daga bisani na kammala a firamaren Bagauda dake Kano. Na yi karatun sakandare a makarantar ‘yammata ta Shekara inda na kammala cikin shekara ta 2000, sannan na yi karatun aikin tsafta a makarantar koyon aikin tsafta ta Kano a shekara ta 2008 daga nan na halarci Kwalejin gwamnatin tarayya dake Kano. Daga nan na tafi jami’a domin fadada ilimi na. Kusan dukkan karatun da na yi, na yi ne a fannin tsafta da kula da lafiya kuma a halin yanzu ina aiki ne a hukumar kula da asibitoci ta Jihar Kano.
Ayyukan kungiyoyi:
Babu shakka na kasance cikin harkokin kungiyoyi tun a shekara ta 1994, inda na zama mataimakiyar jami’ar yada labarai ta kungiyar matan Nijeriya (NCWS) sannan na zama jami’ar yada labarai ta kungiyar kafin daga bisani in zama mataimakiyar shugabar kungiyar ta uku sai kuma na zama mataimakiyar shuaga ta 1 sannan kuma na zamo shugabar kungiyar ta Jihar Kano tun daga shekarar 2011 zuwa yau. Kuma Alhamdulillahi gaskiya muna kokari wajen tabbatar da ganin cewa kungiyoyin mata suna bada tasu gudummawar wajen ci gaban kasa da wanzar da zaman lafiya.
Haka kuma ina cikin wasu muhimman kungiyoyi da suke taka muhimmiyar rawa wajen kyautata zamantakewar al’umma ta fannin kula da lafiya da kuma sana’oi na bunkasa dogaro da kai kamar kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasa watau MAHWUN, wadda ni ce sakatariyar kwamitim mata na kungiyar reshen Jihar Kano sannan ni ce uwar kungiyar mata ‘yan kasuwa ta Jihar Kano kana kuma ni ce ma’ajin kungiyar masu noman rogo ta kasa reshen Jihar Kano , kuma dukkanin wadannan kungiyoyi suna ayyukan inganta rayuwar al’umma ta fannoni daban-daban.
Sauran Abubuwa Na Karin Ilimi:
Na halarci kwasa-kwasai da tarurruka na karin ilimi wadanda hukumomin gwamnati suka shirya tun daga shekara ta 1999 zuwa 2012 a wurare daban-daban , sannan na halarci tarurrukan kara wa juna sani da bitoci wadanda kungiyoyi na duniya suka shirya wadanda lokaci ba zai bari in bayyana su ba saboda yawansu, kuma dukkaninsu sun ba ni cikakkiyar dama na taimakawa al’umma da kuma bauta wa kasa kamar yadda kowane dan kasa yake fatan yi.
kungiyar matan Nijeriya:
Kamar yadda na fada a baya, na fara harkokin kungiya ne tun lokaci mai tsawo, kuma ina matukar alfahari da cewa kungiyarmu ta NCWS tana daya daga cikin kungiyoyin mata da ke bada gagarumar gudummawa wajen kawo ingantuwar al’amurra na zamantakewar al’umma musamman ganin yadda mata suke da muhimmanci ga wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowace kasa ta duniya.
Na jagoranci wani taro mai muhimmanci wanda muka yi a Jihar Katsina cikin shekara ta 2012, kuma alhamdulillahi wannan taro ya yi kyau kwarai domin kuwa an tattauna al’amurra da ke tauye ci gaban kasa da yadda ya kamata mata su bada tasu gudummawar wajen ganin an hada hannu wajen ciyar da kasa gaba. Don haka ko shakka babu kungiyar NCWS tana kokari da gaske domin inganta rayuwar mata a wannan kasa tamu.
Dalilin Shiga Harkokin Kungiyoyi:
Na lura da cewa shiga cikin harkokin kungiyoyi yana kawo ci gaba a kasa, wannan c eta sanya na yanke shawarar shiga cikin kungiyoyi ta yadda zan bada tawa gudummawar tare da abokan aiki kamar yadda muke gani a kasashen da suka ci gaba. Kuma cikin yardar Allah ga shi muna bada gudummawar da za mu iya domin inganta zamantakewa da kuma kyautata hadin kai da taimakon juna .
Shiga cikin kungiyoyi yana bai wa mutane dama su fahimci matsalolin al’umma da yadda zamantakewar al’umma take da kuma yadda za a fuskanci su kansu matsalolin musamman a wannan lokaci da muke ciki ganin cewa akwai dimbin al’umma da suke da tarin matsaloli wadanda kuma suke da bukatar samun wata hanya wadda za su samu saukin wadannan matsaloli dake addabar su.
kalubalen Rayuwa.
To, kalubale kam yana nan kusan a kowane fanni na rayuwar dan Adam, amma yana da kyau mutum ya tsaya ya natsu ya san yadda wadannan kalubale suka faru da matsayin su a zamantakewa da kuma yadda za a fuskance su. Don haka ina mai kara godiya ga Allah Madaukakin Sarki wanda shi ne yake ba ni ikon warware duk wani kalubale da ya same ni ko kuma iyali, sannan yana da kyau mu rika hada wa da juriya da kuma hakuri, rayuwa tana cike da matsaloli wasu ma ba za a iya warware su ba, amma idan ana addu’o i na tabbata za su rika zuwa da sauki kuma za mu rika warware su cikin sauri ba tare da abin ya kai makura ba.
Shawara ga Mata:
Babbar shawarar da nake so in bai wa ‘yan uwana mata ita ce mu cigaba da kare mutuncin mu tare da tsaya wa kan gaskiya a dukkan al’amurranmu mu na yau da kullum, sannan mu sani cewa mu ne iyayen al’umma kuma kada mu yi wasa da neman sana’o I na dogaro da kai ta yadda rayuwar mu da ta iyalinmu za ta yi albarka.
Haka kuma ina mai sanar da ‘yan uwana mata cewa muna da gudummawar da za mu bai wa kasar nan, don haka kada mu bari a bar mu a baya wajen taimakawa kasa da kuma al’ummar kasa ta kowane fanni na zamantakewa. Ina fatan Allah Ya kara mana lafiya da zama lafiya da kuma karuwar arziki a Jihar Kano da kuma kasa baki daya.
Sako Ga Gwamnatoci:
Babu shakka, wajibi ne in yi tsokaci kan gwamnatocin kasar nan dangane da bai wa mata karin dama ta taimakawa kasa domin kamar yadda kowa ya sani, mata muna da amana kuma muna da matukar kwazo wajen bautawa kasa da al’umma. Sannan muna da tausayi a duk inda muka samu kammu, don haka yana da kyau gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kuma na kananan hukumomin kasar nan 774 idan suka kara sanya mata a harkokin gwamnati za a samu ingantaccen ci gaba da yardar Allah.
Bugu da kari, zai yi kyau a baiwa ofishin uwargidan shugaban kasa ya bullo da wani shiri na inganta rayuwar mata kamar yadda aka yi a baya inda matan shugabannin kasa suka yi ta bullo da shirye-shirye na kyautata rayuwar mata wanda gaskiya wadannan shirye-shirye sun yi tasiri ga rayuwar mata, don haka muna kara kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin wannan kasa tamu mai albarka su bai wa matan su damar bullo da shirye-shirye wadanda za su taimaki mata tun daga birane har zuwa yankunan karkara.
Haka kuma ya kamata shirye-shiryen da za a bullo da su su zama na dindindin kuma bisa doka ta yadda kowace gwamnati ta zo za ta tafi da su kamar dai yadda muke gani a sauran kasashen duniya, muddin aka sami wannan tsari, ko shakka babu rayuwar matan kasar nan za ta inganta, kuma kasa za ta bunkasa cikin yardar Allah.
Godiya Ga Abokan Ayyuka
Wajibi ne in jinjina wa abokan tafiyar da harkokin kungiyoyin da nake ciki tare da yaba masu saboda gwagwarmayar da muke sha duk domin ganin matan kasar nan suna samun kulawa mai kyau. Ayyukan kungiya suna da matukar wahala, amma idan aka jure sai a taimaki al’umma a kuma yi mu’amulla ta taimakawa jama’a da mutane iri daban-daban, don haka ina godiya ga ‘ya’yan kungiyar NCWS da shugabannin ta na kasa da na jihohi har ma na yankunan karkara saboda hada hannu da aka yi ana taimakawa mata ta fannoni daban-daban.
Sannan ina godiya ga ‘ya’yan kungiyar ma’aikatan tsafta watau MAHWUN da ‘ya’yan kungiyar mata ‘yan kasuwa da kuma kungiyar manoman rogo saboda ayyukan da muke yi tare batare da nuna kasala ba. Ina fata za mu kara kaimi wajen ganin al’amurra suna cimma nasara duk da halin da ake ciki na tattalin arziki a wannan karni, tared a yin godiya ga dukkanin cibiyoyi da kungiyoyin da suka ba ni lambobin yabo wadanda suke kara min kwarin gwuiwa kodayaushe.
Abin da na fi so:
Gaskiya, ina son karance-karance da tafiye-tafiye na kara ilimi da kuma ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki. Sannan ina sha’awar harkoki na kungiyoyi domin taimaka wa zamantakewar al’umma. Sannan ina son kallon shiry-shirye wadanda suka shafi ilimin kimiyya da kula da lafiya.
A karshe ina amfani da wannan dama wajen godewa maigidana wanda da yardar sa ne nasamu dukkan nasarorin da na samu a rayuwa.