Mata sun fi maza albashi a kamfanonin Saudiyya masu zaman kansu
Albashin mata a kamfanoni masu zaman kan su a Saudiyya ya karu fiye da na maza,. Kamar yadda cibiyar nazarin hada-hadar kudi ta SAMA da ke Saudiyya ta nuna. Albashin mata mafi karanta na kamawa ne daga Riyal dubu uku da 497 wato daidai da Naira 174,850, yayin da maze ke samun mafi karancin albashin […]
Albashin mata a kamfanoni masu zaman kan su a Saudiyya ya karu fiye da na maza,. Kamar yadda cibiyar nazarin hada-hadar kudi ta SAMA da ke Saudiyya ta nuna. Albashin mata mafi karanta na kamawa ne daga Riyal dubu uku da 497 wato daidai da Naira 174,850, yayin da maze ke samun mafi karancin albashin da ya kama daga Riyal dubu biyu da 417 wato daidai da Naira 120,850 .
A shekarar 2015, mafi karancin albashin mata ya karu ne da kashi 3.5 cikin 100 fiye da shekarar da ta gabace ta, inda a da suke daukar Riyal dubu uku da 378.
A Lardin Gabashin kasar mata da maza na samun albashi mai tsoka na Riyal dubu 12 da 085. Can kuwa a Riyadh suna samun gundarin albashin dubu 10 da 430, yayin da a birnin Makkah ake biyan albashin Riyal dubu tara da 166; a Madina ana biyan Riyal dubu takwas da 460.
Sauran biranen kasar da suka hada da Asir mai albashin riyal dubu bakwai da 364; a Tabouka Riyal dubu bakwai da 351; Jouf albashin ya kai Riyal dubu shida da 863; sai Jazan albashin ya kai Riyal dubu shida da 781; kasim ana biyan riyal dubu shida da 674. Can kuwa a garuruwan da ke kan iyakar kasar ta barayin Arewaci, albashin Riyal dubu shida 656, inda a Baha ake biyan Riyal dubu shida da 366, kamar yadda jaridar Okaz ta ruwaito.