Mata sun kama mayakan Boko Haram a Borno
Wasu mata a garin Gwoza da ke Jihar Borno an ce sun kama bakwai daga cikin mayakan Boko Haram da suke addabar garin a ranar Lahadin da ta gabata.Kuma mazauna garin da shaidu sun ce jim kadan da kama su, sai fusatattun matasa da ’yan banga suka yi kwamba suka halaka su.Wasu mazauna garin da […]
Wasu mata a garin Gwoza da ke Jihar Borno an ce sun kama bakwai daga cikin mayakan Boko Haram da suke addabar garin a ranar Lahadin da ta gabata.
Kuma mazauna garin da shaidu sun ce jim kadan da kama su, sai fusatattun matasa da ’yan banga suka yi kwamba suka halaka su.
Wasu mazauna garin da suka tattauna da Aminiya sun jingina nasarar kamun da matan suka yi kan asirin da matan suke da shi.
Majiyoyi a Gwoza sun ce kafin nan wasu mahara sun kwace wata karamar mota dauke da burodi, inda suka yanka mutum hudu da ke cikinta sannan suka tuka motar suka nufi dajin Sambiza. da dama
Motar wadda ke hanyarta ta zuwa Polka daga Gwoza an kai mata hari ne a kauen Warabe.
Wani ganau daga Gwoza wanda ya nemi a sakay sunansa ya ce, “Bayan kwace motar burodin da wasu kayayyaki a Gwoza da kauyukan da ke kusa, sai maharan suka nufi Sambiza inda suka hadu da wasu mata a kan hanya. Maharan sun so su kai hari ga matan, amma sai bindigoginsu suka kasa aiki. Kuma sun yi yunkurin dukansu da gindin bindigoginsu, amma sai dukan hannunwan maharan suka kage, har matasa da ’yan bangar yankin suka cimma masu suka kashe su.”
Shugaban ’yan bangar na Jihar Borno Mohammed Gaba ya tabbatae da aukuwar lamarin, “Lokacin da ’yan bindigar ke fita daga Gwoza, mafi yawan mutane sun gudu don tsira, amma wadannan mata suka ki guduwa. Ina jin maharan sun fusata kuma suka nemi kai musu hari amma suka hadu da karar kwana.” inji shi.