Mata sun yi adddu’a ga ’yan matan Chibok a Jihar Oyo

kungiyoyin mata a Jihar Oyo sun shirya addu’ar musamman kan ’yan matan da aka sace a garin Chibok d ake Jihar Barno. Wannan taron addu’a ya samu wakilci daga kananan hukumomi 33 da ke jihar, wadanda suka hada d akungiyoyin da ba ruwansu da gwamnati.Taron wanda ka gudanar a jiya alhamis, uwar gidan gwmanan jihar, […]

Mata sun yi adddu’a ga ’yan matan Chibok a Jihar Oyo
Mata sun yi adddu’a ga ’yan matan Chibok a Jihar Oyo

kungiyoyin mata a Jihar Oyo sun shirya addu’ar musamman kan ’yan matan da aka sace a garin Chibok d ake Jihar Barno. Wannan taron addu’a ya samu wakilci daga kananan hukumomi 33 da ke jihar, wadanda suka hada d akungiyoyin da ba ruwansu da gwamnati.
Taron wanda ka gudanar a jiya alhamis, uwar gidan gwmanan jihar, Florence Ajimobi ce ta jagorance shi, kamar yadda aka bayar da sanarwa, inda aka yi roko a ’yan boko Haram da su da su bi hanyoyin sasanci, don tabbatar da zaman lafiya.
“Saboda halin firgici da damuwa da muke ciki, muna kira ga wadnanan ’yan tawaye da su bi hanyoyin lalama, su bi tafarkin zaman lafiya. Babu addinin da yake kira a kan tashin hankali, babu addinin da ya yarda da zubar da jini, babu addinin da ya yarda da zubar da jinin wadanda ba su ji ba, ba su gani ba,” a cewar sanarwar.
Tsawon sa’o’i uku da aka ware na wannan adu’a, an umarci ’yan kasuwa da su kulle kantunansu, tun daga takwas na safe zuw karfe 11.
Matan sun yi wannan taron ne a filin wasa na Adamasingba, inda suka kamala addu’o’in sannan suka zarce zuwa gidan gwamnati.