Mata sun yi addu’ar neman saukin matsalar tsaro

Dubun dubatar mata sun yi dandazo domin gudanar da addu’o’in neman sauki daga matsalar tsaro da ta addabi Najeriya. Matan Musulmi da Kirista sun fito kwansu da kwarkwata ne domin yin addu’o’in saboda da yadda matsalar ke kara ci wa Najeriya tuwo a kwarya. “Matsalar tsaro sai daukar sabon salo salo yake a kullum, tana […]

Mata sun yi addu’ar neman saukin matsalar tsaro

Dubun dubatar mata sun yi dandazo domin gudanar da addu’o’in neman sauki daga matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Matan Musulmi da Kirista sun fito kwansu da kwarkwata ne domin yin addu’o’in saboda da yadda matsalar ke kara ci wa Najeriya tuwo a kwarya.

“Matsalar tsaro sai daukar sabon salo salo yake a kullum, tana kuma shafar rayuwarmu, wanda hakan babban kalubale ne ga duk dan Najeriya.

“Dole mu gaggauta komawa ga Allah mu roke Shi Ya kawar mana da wannan fitina, Ya kuma kare mu da lafiya,” inji matar Gwamnan Jihar Osun, Kafayat Oyetola, a wurin taron.

A bayaninta a wurin taron da ya gudana a Gwamnatin jihar, ta ce Najeriya na tsananin bukatar dauki ta bangarori da dama, hakan kuma zai samu ne kawai idan aka koma ga Allah.

“Wannan ya kunshi mu yi aiki tun daga matakin gidajenmu, mu kyutata dabi’ar fifita kudi a kan mutunci; Mu fifita kaunar juna da kyautatawa da aka san kakanninmu da su”, inji ta.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50