Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka
Zanga-zangar na zuwa ne gabanin rantsar da Trump a ranar Litinin.
Dubban mata sun fito zanga-zanga a titunan babban birnin Amurka, Washington DC, domin nuna adawa ga Donald Trump, yayin da ake shirin rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a wa’adi na biyu.
An gudanar da wannan gangamin, wanda aka fara tun 2017, a matsayin abin da aka saba kira “Women’s March” (Gangamin Mata), amma yanzu ana kiransa “People’s March” (Gangamin Jama’a).
Ƙungiyoyi daban-daban ne suka shirya taron domin nuna rashin amincewarsu da manufofin Trump, musamman kan batutuwan sauyin yanayi, shige da fice, ’yancin mata, da haƙƙoƙin baƙaƙe.
A wasu birane kamar New York da Seattle, an kuma gudanar da zanga-zanga don nuna rashin amincewa da manufofin Trump.
Zanga-zangar ta babban birnin Washington ta zo daidai da isowar Trump domin halartar shirye-shiryen bikin rantsar da shi a ranar Litinin.