Mata sun zargi sojoji da kashe mutum 35 a Ribas

A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu matan garin Abonnema da ke Karamar Hukumar Akuku-Toru a Jihar Ribas suka karade titunan garin suna zanga-zangar yin Allah wadai da nuna takaici kan zargin sojojin da aka tura yankin domin tsaro a lokacin zaben Shugaban Kasa da ya gabata da kisan mutum 35 a yankin. Matan sun […]

Mata sun zargi sojoji da kashe mutum 35 a Ribas
Mata sun zargi sojoji da kashe mutum 35 a Ribas

A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu matan garin Abonnema da ke Karamar Hukumar Akuku-Toru a Jihar Ribas suka karade titunan garin suna zanga-zangar yin Allah wadai da nuna takaici kan zargin sojojin da aka tura yankin domin tsaro a lokacin zaben Shugaban Kasa da ya gabata da kisan mutum 35 a yankin.

Matan sun karade garin Abonnema sanye da bakaken kaya suna fadin ba su yarda da kisan da sojojin da aka turo yankin lokacin zabe suka yi ba, kuma ba su yarda su kara zuwa domin ci gaba da yi musu kisan gilla ba.

Da take yi wa manema labarai karin bayani, jagorar zanga-zangar, Tonye Briggs-Oniyinde ta ce ba za su kara yarda gwamnati ta sake turo soja yankinsu ba a zaben Gwamna da za a yi gobe Asabar. “Domin har yanzu muna zaman makokin kisan ’yan uwa da ’ya’yanmu da sojoji suka yi mana. Har yanzu kuma muna neman ragowar gawarwarkin da ba mu gani ba,” inji ta.

Briggs, wadda ’yar Kwamishinan Al’amuran Yawon Shakatawa na Jihar Ribas ne, ta ci gaba da cewa “Har yanzu hankalinmu ba kwance yake ba mu ’yan kabilar Kalabari saboda wannan al’umma ba ta taba ganin irin tashin hankalin da ta gani lokacin zaben Shugaban Kasa ba, don haka mu daukacin iyaye muke bakin ciki da wannan abu.”

Ta ce sama da mutum 35 aka kashe a lokacin zaben. “Wannan al’umma kowa ya san cewa mu mutane ne masu son zaman lafiya kuma lafiya lau muke zaune da kowa,” inji ta.

Haka matan sun bukaci sarakunansu  su samar masu da mafita daga wannan al’amari na kisan ’ya’yansu, don kada hakan ya sake faruwa.

A jawabinsa na lallashi Sarkin Abonnema, Amanyanabo na Abonnema, Cif Disrael Gbobo Bob-Manuel ya bukaci matan su kwantar da hankalinsu, su koma gidajensu. Ya ce sarakunan yankin na nan sun hada karfi da karfe suna tattauna yadda za a shawo kan lamarin, har a kai ga warware shi. “Ni ba zan zuga ku daukacin kabilar Kalabari ku zama sususu ba, amma yana da kyau kuma ku tashi tsaye domin wannan al’amari ya wuce tunaninmu,” inji shi.

Sarki Bob-manuel ya kara da cewa “Ko lokacin da aka yi Yakin Basasar kasar nan, muna nan ba inda muka matsa amma ba mu taba ganin irin yadda aka dauki ran dan Adam kamar kiyashi ba sai a wannan karo a masarautar Abonnema ta Kalabari.”