Mata ta kashe mijinta a kan Naira dari

Wata matashiya mai suna Gift Wahab, mai shekaru 20 a duniya ta kashe mijinta mai sun a John Amazu mai shekaru 28 da haihuwa ta hanyar daba masa wuka a wuya yayin da suke fada a kan Naira dari daya ta cefe ne a Jihar Legas. Aminiya ta gano cewa lamarin ya auku ne a […]

Mata ta kashe mijinta a kan Naira dari
Mata ta kashe mijinta a kan Naira dari

Wata matashiya mai suna Gift Wahab, mai shekaru 20 a duniya ta kashe mijinta mai sun a John Amazu mai shekaru 28 da haihuwa ta hanyar daba masa wuka a wuya yayin da suke fada a kan Naira dari daya ta cefe ne a Jihar Legas.

Aminiya ta gano cewa lamarin ya auku ne a gida mai lamba 24 da ke kan titin Fasasi a unguwar Ajegunle a kwanakin baya da misalin karfe 10 na safe.
Da take yin karin bayan kan yadda lamarin ya auku, Gift ta bayyana cewa tsautsayi ne ya sa ta kashe mijin nata.
“Lamarin ya auku ne da misalin karfe goma na safe. Zan tuna a lokacin ba na iya ganin irin raunin da na yi masa saboda halin galabaita da nake ciki, sakamakon dukan kawo wuka da ya yi mini. Idan da a ce na san cewa zai mutu da ban dauki wukar ba. Wato abin da ya faru shi ne, mun fita yawo sai muka zauna a wata mashaya da ke kusa da gidanmu a nan ya sha giya, ni kuma na gaji, sai na ce masa ya ba ni mukulli na tafi gida, sai ya ce ba zai ba ni ba yunwa yake ji, sai na ce masa zan ririta sauran Naira dari daya da muke da ita har zuwa gobe, sai ya kama fada yana zagi na yana cewa kada na sake fadar cewa Naira dari ce ta rage mana. Sai muka fara cacar baki, kawai ya kama dukana har ya yi mini rauni a hanci. Jini ya rika zuba, sai na fito waje, sai wani mutum ya ba ni hankicinsa na tsayar da jinin ya ce mini na tafi gida na balle mukullin kofar na kwanta, sai ya biyo ni har gida yana duka na, ni kuma saboda ganin ya fi karfina ban san lokacin da na dauko wuka na caka masa a wuya ba, jim kadan sai na ji cewa wai ya mutu,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa: “Da ma ni na saba kusan kullum sai ya dake ni, har mai gidan da muke yin haya ta gaji ta ce idan ta sake ji mun yi fada sai ta tashe mu, daga nan sai muke yin fada cikin sirri. A yanzu haka zancen da nake yi ina da cikinsa. Akwai ’yan uwansa da suka zo suka rika duka na suna cewa sai sun kashe ni su ma kamar yadda na kashe dan’uwansu. Da kyar aka kwace ni.”
Sai dai kotun gargajiya da ke unguwar Ebute Meta ta bayar da umarnin a ci gaba da ajiye Gift a gidan yari har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron shari’ar a watan gobe.
Binciken Aminiya ya gano cewa Gift ’yar asalin kabilar Ishan ce da ke Jihar Edo, shi kuwa mijinta John dan kabilar Ijaw ne da ke Jihar Delta kuma sun hadu a unguwar Ajegunle har suka yi aure.
Gift ita ce ta farko a wurin iyayenta shi kuwa John ya rasa aikinsa tun shekaru biyu da suka gabata.