Mata ta mari mijinta don ya ladabtar ta ’ya’yansu
Wani magidanci ya yi karar matarsa yana neman a raba aurensu saboda tana marin sa duk lokacin yake ladabtar da ’ya’yansu. Mutumin ya fada wa kotun Kotun Kwastomari da ke Mapo a Ibadan, Jihar Oyo cewa matar tasa d suka shekara 14 tare tana zabga masa mari ne kawai saboda yana hora yaran su hudu […]
Wani magidanci ya yi karar matarsa yana neman a raba aurensu saboda tana marin sa duk lokacin yake ladabtar da ’ya’yansu.
Mutumin ya fada wa kotun Kotun Kwastomari da ke Mapo a Ibadan, Jihar Oyo cewa matar tasa d suka shekara 14 tare tana zabga masa mari ne kawai saboda yana hora yaran su hudu don su gyara halinsu su daina rashin ji.
- An yankewa wani ma’aikaci hukuncin kisa ta hanyar rataya
- An rufe bankuna uku a Maiduguri
- Ba a sako Daliban Kagara ba —Gwamnan Neja
“Matata kwata-kwata ta tarwatsa hadin kanmu, tana nuna wa yaran tsananin so.
“Duk lokacin da nake ladabtar da daya daga cikinsu saboda rashin ladabi takan goyi bayanshi ta kuma kifa min mari.
“Ba ta da ladabi da biyayya ,” inji shi.
Matar wadda ’yar kasuwa ce, ta bukaci da mijin nata ya sawwake mata, ya sake ta.
Ta bayya wa kotu cewa, “Mijina kazami ne, ba ya wanke tufafinsa ko jikinsa bayan ya cakudu da dabbobin da ke gidan.
“Eh, tabbas na mare shi saboda ya dake ni kan ya ce min na bar masa gidansa.
“Kwata-kwata bai iya soyayya ba, sam ba na son shi,” inji ta.
Alkalin kotun, Mai Shari’a, Ademola Odunade, ya ce za su iya ci gaba da zamansu a matsayin miji da mata muddin za su iya hakuri da junansu.
Odunade, ya bukaci ’yan uwan ma’auratan daga kowane bangare da su shigo cikin lamarin don samar da sulhu a tsakaninsu.
Alkalin kotun ya kuma dage zaman kotun zuwa ranar 6, ga watan Afirilu don ci gaba da sauraren karar.