Mata ta na kokarin auren wani a boye, inji mijin da ke neman saki a kotu
Ya yi zargin cewa saurayin da take son ta aura ne yake turo mata da kudi domin shirye-shiryen auren nasu.
Wani miji mai suna Moses Ojo ya roki Kotun Majistare dake yankin Jikwoyi na Babban Birnin Tarayya Abuja da ta raba aurensa da matarsa saboda ya ce tana kokarin sake auren wani mijin ba tare da saninsa ba.
A karar da ya shigar mijin, wanda ma’aikacin gwamnati ne ya yi zargin cewa matar tasa mai suna Martha ta jima tana cin amanarsa ta hanyar tafiye-tafiye ba tare da izininsa ba.
- Mai ’ya’ya 8 na neman a raba aurenta na shekaru 19 saboda rashin abinci
- An kama limamin da ya daura wa gawa aure a Bauchi
Ya yi zargin cewa saurayin da take son ta aura ne yake turo mata da kudaden mota domin su ci gaba da shirye-shiryen auren nasu.
“Martha ta jima tana barazanar kashe ni saboda ta ci gado na,” inji shi.
Kazalika, mai karar ya kuma shaidawa kotun cewa tun da farko sai da ya kai kararta zuwa wajen iyayenta wadanda suka ba shi shawarar rabuwa da ita.
To sai dai a iya tsawon lokutan sauraron karar, matar ba ta halartar zaman kotun kuma ba ta taba turo wakilci ko wasika a kan dalilin rashin zuwan nata ba.
Daga nan ne sai alkalin kotun, Mai Shari’a Jamilu Jega ya dage ci gaba da zaman kotun har zuwa ranar 26 ga watan Janairun 2021 domin a ba matar damar bayyana gaban kotun domin ta kare kanta.