Mata ta sheka wa mijinta tafasasshen ruwa a Kano
Matar ta ce aure dole aka yi mata da mijin nata.
Watar matar aure ta antaya wa mijinta tafasasshen ruwa saboda wata takaddama da suka samu tsakaninsu a garin Kano.
Magidancin da a halin yanzu yake a kokkone yana zaune tare da matar tasa ce a yankin Unguwa Uku.
- Yunwar Wata 9 Ce Ta Sa Mu Yajin Aiki —Likitoci
- Abin da ya sa ’yan bindiga ke tursasa matan da suka kama auren su
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
Bayan an tsare ta sakamakon aika-aikan, matar mai shekara 17, ta ce da ma can sai da ta fada wa mahaifanta cewa ba ta son shi, amma suka yi mata auren dole da shi.
A cewarta, tun bayan daurin auren take ta fama da matsaloli a gidan nasa, ba kuma ya ciyar da ita, ballantana ta samu kulawar daga gare shi.