Mata ta yanke mazakuntar mijinta ta ba kare ya cinye
’Yan sandan a kasar Ukraine sun ce wata matar aure ta yanke mazakuntar mijinta bisa zargin ya dauki shekaru yana wahalar da ita a zaman aurensu. Matar da ake tuhuma mai suna Maria mai shekara 48 bayan yanke mazakuntar mijin sai ta jefa wa karen gidansu a matsayin abinci a kauyen Obarib a Arewacin kasar. […]
’Yan sandan a kasar Ukraine sun ce wata matar aure ta yanke mazakuntar mijinta bisa zargin ya dauki shekaru yana wahalar da ita a zaman aurensu.
Matar da ake tuhuma mai suna Maria mai shekara 48 bayan yanke mazakuntar mijin sai ta jefa wa karen gidansu a matsayin abinci a kauyen Obarib a Arewacin kasar.
Maria, ta bayyana wa ’yan sanda cewa, ta dade tana shan ukuba a hannun mijinta a tsawon shekaru don haka ta yanke shawarar kai karshen wannan wahala da take sha a wajen mijin.
Maria, ta yanke wa mijinta mai suna Oleksandr, mai shekara 49 mazakutarsa ce a lokacin da yake kwance a dakinsa bayan ya dawo daga aiki, inda barci ya dauke shi a safiyar ranar 23 ga watan Agustan bana.
Matar ta kuma kashe mijinta, inda ta yi amfani da gatari wajen sare kan Oleksandr, kamar yadda ’yan sandan suka sanar.
A cewa wata kafar labarai ta kasar garin cewa, bayan Maria, ta sare kan mijin sai ta dauki wukar girki ta yanke mazakuntarsa sannan ta bai wa karen gidansu a matsayin abinci.
Da farko ta yi yunkurin yanka sassan jikin Oleksandr, amma abin ya ci tura, kamar yadda binciken da aka gudanar ya nuna.
Bayan Maria, ta aikata wannan aika-aikar sai ta shafa jinin jikin mijin nata a jikinta, ta nufi gidan wata makwabciyarta mai suna Misis Nadezhda Opanasiuk.
Misis Nadezhda, ta bayyana wa kafar labaran cewa, “Hannuwan Maria da kafafunta da rigar jikinta duk jini. Tana cewa, ina cikin matsala na kashe mijina.”
Sai Misis Nadezhda, ta ce ban yarda da abin da take fada ba, na yi zaton ko suna fada da mijin ne, ta buga masa wani abu, sai na fara tunanin ko mijin na bukatar taimakon magani ne.
“Da na shiga dakin Oleksandr, sai ga gawarsa cikin jini, zanen gadon dakin ya jike da jini. Sai na tambayi Maria, ina kan mijinki? Sai ta amsa da cewa, ga shi can cikin buhu,” inji Misis Nadezhda.
Ta ce Maria ta yi shiru kamar ba ta da lafiya, sai wasu makwabtan gidan suka yi gaggawar kiran ’yan sanda.
Maria, ta amsa laifin kisan mijinta bayan jami’an tsaron sun tsare ta, sannan ta yi musu cikakken bayani game da abin da ta aikata.
Kakakin ’Yan sandan, Badim Artiukhobich ya ce: “Wanda ake tuhuma ta yi bayanin cikakken abin da ya faru, an tabbatar da ta aikata laifin kisan kai, don haka aka a jiye ta wajen wadanda suka aikata laifin kisan kai.”
Ita dai matar ta ce, ta aikata haka ne kawai sakamakon wahalar da take sha a zaman auren da suke yi da mijinta kuma ta ga abin da ta aikata kawai shi ne mafita.
Makwambtan Maria, sun tabbatar da cewa mijinta lokaci da dama yana bin ta da bulala yana duka wani lokaci har ma da gatari. Wannan mata ba ta taba kai karar mijin ba, duk da irin wahalar da take sha a wajensa.
Dan Maria, mai suna Biktor Fesianob, ya ce ba zai yafe wa mahaifiyarsa ba game da abin da ta aikata.
Biktor ya kara da cewa, “Na sani mahaifiyata ce, amma yanzu ba na bukatar ganinta har abada.“ Kamar yadda kafar labaran ta ruwaito.
A yanzu haka idan aka tabbatar da laifin za a yanke wa Maria, daurin shekara 15 a gidan yari, kuma ana ci gaba da bincike kan lamari.