Mata ta zargi mijinta da sace gawar dansu

Sai ya kawo gawar kafin in yarda a raba aurenmu da shi.

Mata ta zargi mijinta da sace gawar dansu

(Getty Images)

Wata matar aure da mijinta ke neman rabuwa da ita ta ce ba za ta amince ba sai ya kawo mata gawar dansu. 

Ta kalubalanci mijin nata ya kawo gawar dan nasu ne a matsayin sharadinta na amincewa a raba auren bayan mijin ya bayyana wa kotu cewa son da yake mata a baya ya gushe.

Matar ta shaida wa Kotun Kwastomari da ke zamanta a Igando, Jihar Legas cewa mijin nata “Ya dauki gawar danmu daya tal da muka haifa ya yi batan dabo. Ban san abin da ya yi da gawar ba.

“Ya kawo min gawar da na shi ne kadai sharadin amincewata a raba aurenmu da shi.

“Na ci wuya tare da fama da cututtuka iri-iri tun bayan bacewar dan namu. Bai zai ci moriyata sannan ya yi watsi da ni ba,” inji ta.

Sai dai a bayaninsa, mijin ya shaida wa kotun cewa babu son matar tasa a ransa a yanzu.

“Son da nake wa matata a baya ya gushe, ina so kowa ya kama gabansa, a raba mu; Ta bar min gidana ta ba ni mukullaina.” inji shi.

Shugaban Kotun, Adeniyi Koledoye, ya dage zaman zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2021 domin yanke hukunci.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya