Mata uku ’yan Hisba sun rasu a hadarin mota

A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi rashin ma’aikatanta mata uku, wadanda suka rasu a hadarin mota a dajin Falgore da ke karamar HukumarDoguwa da ke jihar. Darakta Janar na Hukumar Hisba, Abba Sa’id Sufi ya shaida wa Aminiya cewa ma’aikatan sun rasu ne a kan hanyarsu ta […]

Mata uku ’yan Hisba sun rasu a hadarin mota
Mata uku ’yan Hisba sun rasu a hadarin mota

A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi rashin ma’aikatanta mata uku, wadanda suka rasu a hadarin mota a dajin Falgore da ke karamar Hukumar
Doguwa da ke jihar. Darakta Janar na Hukumar Hisba, Abba Sa’id Sufi ya shaida wa Aminiya cewa ma’aikatan sun rasu ne a kan hanyarsu ta zuwa duba yanayin zamantakewar sababbin ma’auratan da hukumar ta aurar kwanakin baya. “Kamar yadda al’adar hukumar take a duk lokacin da muka aurar da amare, mukan kafa kwamitin da yake bibiyar yanayin zamantakewarsu, koda za a samu wata matsala sai mu yi sulhu. To irin wannan fitar ce wadanan mata suka yi, inda suka fara wannan zagaye a ranar 18 ga wannan wata, sun kamala da kananan hukumomi 36, kanaann hukumomin cikin birni ne kawai suka rage musu,” inji shi. Darakatan ya ce hukumarsu za ta dade tana jimamin rashin wadanan ma’aikata saboda jajircewarsu wajen aiki. Daga cikin wadanda suka rasu akwai Hadiza Aliyu Jibril da Maryam Musa Abdulalhi (Saukakkiya) da Hafsa Mohammad, kuma an ce kowaccensu ta rasu ta bar mijinta yara da kuma ’yan uwa. An yi jana’izarsu kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada inda aka yi musu Sallah a kofar Gidan Sarkin Kano.