Mata ’yan Shi’a sun yi zanga-zangar a sako Zakzaky

Ranar Talatar da ta wuce ne mata ’yan Shi’a suka yi zanga-zangar lumana suna neman a su sako shugabansu Sheikh Ibrahim Zakzaky da mazajensu da aka kama kwanakin bayan rikicinsu da soji a Zariya. Matan sun ce an kashe mazajen mata da yawa tare da mayar da ’ya’yansu marayu kuma suna bukatar a sako dukkan […]

Mata ’yan Shi’a sun yi zanga-zangar a sako Zakzaky
Mata ’yan Shi’a sun yi zanga-zangar a sako Zakzaky

Ranar Talatar da ta wuce ne mata ’yan Shi’a suka yi zanga-zangar lumana suna neman a su sako shugabansu Sheikh Ibrahim Zakzaky da mazajensu da aka kama kwanakin bayan rikicinsu da soji a Zariya. Matan sun ce an kashe mazajen mata da yawa tare da mayar da ’ya’yansu marayu kuma suna bukatar a sako dukkan wadanda suke tsare ba tare da wata ka’ida ba.
Wadanda suka yi zanga-zangar sun zargi sojoji da cin zarafi da rashin mutunta dan Adam, tare da yunkurin kawar da zuriyarsu daga dorar kasa.
Shugaban Matan A’isha Hassan ta ce, “Sojojin sun haka rami sun binne wadanda suka kashe, kuma sun kone wasu gawarwaki na mata da maza wasu matan ma sai da sojojin suka yi musu fyade kafin su kashe su. Mun kuma samu wannan bayani ne daga bakin matan da suka tsira a lokacin rikicin.” Ta kara da cewa “Muna sane da cewa abin da sojojin suka yi wani shiri ne na a tunzura mu domin mu ta da fitina kamar abin da ya faru a bara, inda sojojin suka hallaka ’ya’yan Sheikh Zakzaki uku tare da kashe mutanenmu 34, ga shi yanzu sun sake kashe masa ’ya’ya uku amma har yanzu mun danne zukatanmmu.” Ta yi kira ga Rundunar Soji ta biya su diyyar rayukan da jami’anta suka hallaka, sannan su sako ’yan uwansu da ke tsare.