Mata ’yan siyasa su ne matsalar kansu
Hajiya A’isha Haruna Kabuga tsohuwar ta taba tsayawa takarar kansila a karamar Hukumar Gwale a karkashin Jam’iyyar APC, a tattaunawarta da Aminiya ta bayyana rashin hadin kai a tsakanin mata ‘yan siyasa a matsayin babbar matsalar da ke kawo rashin nasararsu a siyasa. Ta ce hakan ya sa suka kafa kungiyar ’yan takara mata don […]
Hajiya A’isha Haruna Kabuga tsohuwar ta taba tsayawa takarar kansila a karamar Hukumar Gwale a karkashin Jam’iyyar APC, a tattaunawarta da Aminiya ta bayyana rashin hadin kai a tsakanin mata ‘yan siyasa a matsayin babbar matsalar da ke kawo rashin nasararsu a siyasa. Ta ce hakan ya sa suka kafa kungiyar ’yan takara mata don su gudu tare su tsira tare:
Aminiya: Me ya ja hankalinku kuka kafa kungiyar mata ’yan takara?
A’isha Kabuga: Bayan mun fito takara ba mu yi nasara ba, sai na ga akwai bukatar mata irina mu hadu wuri guda don mu tafi tare don cimma burinmu. Hakan ya sa muka kafa wannan kungiya, kuma
kungiyar babu ruwanta da bambancin jam’iyya. A cikinmu akwai ’yan APC da PDP da sauran jam’iyyun siyasa. Mun kafa ta a matakin jiha, yanzu muna kokarin fadada ta yadda za ta zama ta kasa. Manufarmu ita ce mu zaburar da ’yan takara mata da kada su ja baya a neman mukaman da suke yi. Haka muna da manufar son ganin idan mace ta fito takara ya kamata ta tsaya ta jajirce har sai ta kai ga nasara. Idan ta fadi zabe kada ta fitar da rai muna so haka ya zame mata kamar allura yadda za ta ji cewa gobe ma idan an buga gangar siyasa za ta sake fitowa takara. Tun tana fitowa tana faduwa mun yi imani wata rana za ta samu nasara. Me nema yana tare da samu. Baya ga matan da suka taba tsayawa takarar siyasa, su kansu matan da suke sha’awar tsayawa takarar sun shigo cikinmu muna wannan tafiya tare da su. A yanzu haka a shirye suke da zarar zaben shekarar 2019 ya tunkaro za su fito da karfinsu su tsaya takara.
Aminiya: Wace matsala mata ’yan siyasa ke fuskanta?
A’isha Kabuga: Baya ga matsalar da muke fuskanta daga wurin maza inda suke kokarin take mu ta kowace hanya a wajen neman mukamai, a gefe guda kuma mu kanmu matan mukan yi wa junanmu hasada. Ba ma son mu ga wata a cikinmu ta fi mu samun nasara. Akwai abin da ya faru a wata karamar hukuma bayan wata yar takara ba ta yi nasara ba, sai a aka yi kokarin ba ta wani mukami na wakilci, a nan sai wata ’yar siyasa ta zaburo ta ce ba ta yarda ba, a ganinta ita ta fi dadewa a harkar siyasa. A karshe dai haka aka yi asarar mukamin babu wacce ta samu a cikinsu, suna ji suna gani maza ne suka samu mukamin.
Aminiya: Kina ganin mata sun cika burinsu na samun kashi 35 na mukamai a wannan gwamnati?
A’isha Kabuga: Alhamdulillahi wannan gwamnati ta ba wa mata da yawa mukamai. Tun daga kan mukaman kwamishinoni da manyan daraktoci da mashawartan Gwamna da sauransu, mukamin Kwamishinan Kasafi da Tsare-Tsare da aka fi ba wa maza, a wannan karon mace aka ba wa. Amma duk da haka muna neman kari, muna neman a ba mu dama sosai a manyan mukaman gwamanti.
Aminiya: Wane kira kike da shi ga mata ’yan siyasa?
A’isha Kabuga: Ina kira gare su da mu hada kai mu kuma rika goya wa junanmu baya a duk lamurran da muka sa gaba na ci gaban siyasa. Idan aka samu hadin kai a tsakaninmu, to maza za su ji shakkar ci mana dunduniya. Akwai bukatar mu tallafa wa junamu ta kowace hanya. Ina kira ga mata mu fito mu nemi mukaman siyasa tun daga kan kansila zuwa ciyaman zuwa gwamna da dan majalisa da sanata. Idan kun duba mata ne ke fitowa kada kuri’a, don haka in dai har an samu hadin kai a tskaninmu, to ba shakka za mu samu nasara, matan nan za su fito su zabe mu.
Aminiya: Wane kira kike da shi ga gwamnati?
A’isha Kabuga: Muna kira ga gwamnati cewa ta rika yin la’akari da mu mata musamman wadanda suka fito takara. Idan mun samu nasarar cin zabe, alhamdulillah. Idan kuma ba mu samu ba, to muna neman ta rika ba mu mukami na wakilci, musamman kujerun mataimakan shugabanni da sauransu. Za ki ga a jihohin Kudu har mukaman mataimakan gwamna an ba wa mata. Mu dama burinmu na shiga siyasa tare da neman mukami shi ne don mu taimaki mata ’yan uwanmu rayuwarsu ta inganta. Kasancewar maza ne a kan mukaman gwamnati sai ki ga matan ba su samun sakewa su gaya musu matsalarsu. Amma idan mata ne a mukaman fa, da gudu za su je su gaya musu matsalarsu. Ko ba komai ciwon ’ya mace na mace ne. Ya kamata gwamnati ta fahimci cewa mu mata mu ne muka san matsalolin mata da matasa, don haka mu ne muka fi cancanta mu yi musu magani. Idan aka ba wa mace mukami ana samun abin da ake nema, kasancewar mata sukan jajirce wajen sauke aikin da aka dora musu. Kuma ko batun cin hanci da ake yi, na tabbata ba za a samu mata da irin wannan harkar ba, kasancewar mata suna da tsoron fadawa cikin badakala. Idan kuwa haka ne ashe mu mata muka fi cancanta a ba mu mukamai.