‘Mata za su iya bayar da gudummuwa wajen yaki da cin-hanci’
A kwanakin baya ne Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya yi kira ga mata cewa kada su karbi kudin sata daga mazajensu. Wannan ya sa Aminiya ta tattauna da Amirah kungiyar Mata Musulmi ta FOMWAN reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, Hajiya Maryam Aliyu Abdullahi, kan ko mata za su iya bayar da gudummuwa […]
A kwanakin baya ne Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya yi kira ga mata cewa kada su karbi kudin sata daga mazajensu. Wannan ya sa Aminiya ta tattauna da Amirah kungiyar Mata Musulmi ta FOMWAN reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, Hajiya Maryam Aliyu Abdullahi, kan ko mata za su iya bayar da gudummuwa wajen kawo karshen cin- hanci da rashawa a kasar nan. Ga yadda hirar ta kasancAminiya: Shin ko mata za su iya taimakawa wajen kawo karshen cin-hanci da rashawa, kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara yaki da hakan?
Hajiya Maryam: Wani lokacin mu mata muke janyo ma kanmu wahala har mu kai ga halaka iyalanmu. Kuma ba komai ke kawo wannan ba illa gasa, mata mun cika gasa, a ce duk abin da wancan ta yi ni ma sai na yi, kuma yana yiyuwa samun mazajenku ba daya ba ne, idan kika matsa wa mai gidanki, zai sa shi cikin wani hali har ya janyo masa fara nema ta hanyar da ba ta dace ba don dai ya biya miki bukatarki.
Don haka mu, mata muna da rawar da zamu iya takawa don kawo karshen wannan bala’in da ya addabi kasarmu Najeriya, ka ga mutum da ya yi aiki yana neman a dan ba shi wani abu duk da ya san za a biya shi.
Idan mata zasu iya ja ma kansu kunne ta hanyar nuna cewa fa duk wata wahalar duniya mai karewa ce wanda za mu iya jure mata, amma kuma lahira har abadan ce, azabar ta mai radadi ce. Don haka mu rika yiwa mazajen mu wa’azi kullum, kamar yadda matan sahabbai suke yi, mu rinka lurar da mazajen mu aibin cin-hanci da rashawa da abin da yake haifarwa, mu zama masu wadatar zuci, mu bar gasa, mu dauka duk wani abu yin Allah ne, mu zama masu yin jagorancin ’ya’yanmu ta hanya madaidaiciya.
Ina mai tabbatar mi ki da cewa idan mata suka tashi tsaye wajen taimakawa Shugaban kasa Buhari, wajen wannan yaki da cin-hanci da rashawa, za a yi nasara, domin duk al’ummar da matan ta suka gyaru insha Allahu komai zai yi dai dai, mu mata mu ne komai, don haka ina son na yi amfani da wannan damar don yin kira ga mata ’yan uwana, da mu ji tsoron Allah, mu toshe son zuciya, mu bi Allah da Annabinsa Muhammad (SAW), mu nisanci haramun, mu rungumi halal don tsirar da kanmu da ’ya’yanmu.
Aminiya: Ko za ki bayyana mana matsayin cin-hanci da karbar rashawa a addinin Musulunci?
Hajiya Maryam: Da farko dai cin-hanci da rashawa a Musulunci haramun ne, Allah Ya hana, bala’i ne ga kasa. Allah (SWT) Ya hana kuma duk abin da Allah ya haramta mana mafi alheri dare mu shi ne mu nisance shi, amma yau sai aka wayi gari mutane sun mayar da shi ba kan komai ba, har ya bi jini, duk abin da a ka ce Allah Ya hana, idan ka ce zaka yi sai ya zama babban masifa, a mastaya na ina mace, ina ba ’yan uwa na mata-shawara, kai kar da mazan, guje wa wannan dabi’ar.
Mutum yana iya rayuwa ba tare ya yi cin-hanci da karbar rashawa ba. A zamaninsu Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa balewa da sauransu, a lokacinsu ba a san cin-hanci ba, sun yi mulki kan gaskiya da. Abin nufi a nan shi ne sun san duniyar nan ba wurin dawwama ba ne, don haka ba su dauki duniyar nan kan komai ba gashi har yau ana tuna irin kyawawan ayyukkan da suka yi, a lokacin su abin kunya ne, a ce yau gashi mutun ya ba da cin-hanci, amma a zamanin nan namu an mayar da cin-hanci abin ado, wasu har yaba wa kansu suke ana alfahari.
Aminiya: Ina mafita?
Hajiya Maryam: Ni yanzu shawara ta ga al’umma Musulunci da wadanda ba Musulmi ba, shi ne, aji tsoron Allah, a tuna akwai mutuwa da tashin kiyama, wanda babu makawa akwai hisabi, za mu iya rayuwa ba tare da mun yi wadannan miyagun ayyuka ba mutum ya tsara rayuwarsa ta hanyar da yasan ba zai samu kasa wa a samun sa ba, a tsanake, misali, idan mutum ma’aikacin gwamnati ne ana ba shi albashi wata-wata ya cire kudin sutura, na abinci, kula da yara da makarantarsu, na taimakon dangi da abokan arziki da na ajiya don lalurar rashin lafiya ko wani abu da yakan iya faruwa wanda ba a hasashensa, da haka ba ka cikin samun karanci daidai ruwa daidai kurji.
Lokacin da rigimar ke tasowa shi ne, idan Allah Ya aje matum wani mataki, sai shi ya ce shi ba zai tsaya nan ba, sai a yi ta nema ta hanyar da Allah Ya haramta daga karshe a zo ana nadama.