…..Mata za su kai wa Buhari da mataimakinsa Alkur’ani da Bibul

A yayin da mutane ke cigaba da yin tattaki daga garuruwa daban-daban zuwa Abuja a kasa domin nuna farin cikinsu ga nasarar cin zaben Janar Muhammadu Buhari, a ranar laraban nan kuma wadansu matasu goma, musulmi da kirista, suka kama hanyar zuwa Abuja daga Kaduna domin nuna nasu farin cikin. A cewar matan, za su […]

…..Mata za su kai wa Buhari da mataimakinsa Alkur’ani da Bibul

A yayin da mutane ke cigaba da yin tattaki daga garuruwa daban-daban zuwa Abuja a kasa domin nuna farin cikinsu ga nasarar cin zaben Janar Muhammadu Buhari, a ranar laraban nan kuma wadansu matasu goma, musulmi da kirista, suka kama hanyar zuwa Abuja daga Kaduna domin nuna nasu farin cikin.

A cewar matan, za su yi tattakin ne domin su mika wa zababben shugaban kasa Janar Buhari kyautar Alkur’ani, shi kuma mataimakinsa Osinbajo su ba shi Bibul.
Matan sun fara tafiyar ne da misalin karfe 9:30 na safe daga filin makarantar firamare ta Unguwar Ma’azu da ke Kaduna.
Da take amsa tambayoyin manema labarai a kan dalilinsu na yin wannan tattakin duk da wahalarsa, Malama Bilkisu Ibrahim ta ce za su je ne su mika wa Buhari da mataimakinsa Alku’rani da Bibul da zarar sun isa Abuja. “ Mun shirya yin wannan tafiyar ce domin nuna farin cikin samun canjin gwamnati da aka yi a kasar nan. Kuma a matsayinmu na ‘yan Najeriya kuma mata, muna son nuna wa wannan gwamnati cewa mata ma sun zabe ta kuma ya kamata a kula da ‘yancinmu a kasar nan. Muna kaunar wannan kasa da kuma hadin kan ‘yan kasar nan, shi ya sa a wannan tafiya tamu akwai mata musulmi da kiristoci domin mu nuna wa shugaban kasa Buhari cewa akwai hadin kai a kasar nan, don haka ya mulke mu da adalci da gaskiya,” inji ta.
A cewarta, sun aika da wasika ga kwamishinan ‘yan sandan jahar Kaduna kafin su fara tafiya, inda kuma aka shawarce su da kada su yi tafiyar a cikin dare.
Haka nan kuma ta ce sun bukaci taimakon jami’an Hukumar kiyaye hadura, wadanda suka amince za su rufa masu baya har zuwa Abuja.
Malama Bilkisu sai ta yi kira ga Janar Muhammadu Buhari da ya kawo cigaba mai ma’ana ga kasa domin a cewarta, jama’ar kasar nan sun wahala matuka a hannun gwamnati mai wucewa.