Mata zaman banza ba namu ne ba- Hajiya Maryam Lawal Rumah
Takaitaccen tariyin rayuwa:Ni ’yar asalin Jihar Adamawa ce. An haife ni a Mubi a 1967. Na yi makarantar firamare a Yalwa. Na je sakandaren Gwamnati da ke Jalingo. Daga nan na yi aure, na tafi da mijina kasar Amurka, na yi shekara daya na dawo. Na yi difloma a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna […]
Takaitaccen tariyin rayuwa:
Ni ’yar asalin Jihar Adamawa ce. An haife ni a Mubi a 1967. Na yi makarantar firamare a Yalwa. Na je sakandaren Gwamnati da ke Jalingo. Daga nan na yi aure, na tafi da mijina kasar Amurka, na yi shekara daya na dawo. Na yi difloma a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna ( Kadpoly) kan Tsara Birane (Regional Planning). Na sake komawa Amurka, na yi Babbar Diploma (Adbance Diploma). Bayan nan Allah Ya yi wa mijina rasuwa na dawo Najeriya, na kara yin aure. Ina da ’ya’ya biyu, Hannatu da Sayyib.
Ilimin mata a Arewacin Najeriya:
A gaskiya ilimin mata a Najeriya yana baya. Lallai sai mun tashi tsaye don mu yi gyara sosai. Mu da muka yi karatu, muka je wurare da dama a duniya, kowa ya yi nasa kokarin don ganin an samu ci gaba, domin kuwa ilimi shi ne ginshikin komai na rayuwa. Dalilin wannan aiki nawa -saboda shi na karanta a makaranta, kuma ina da ra’ayin yin haka, ta dalilin haka ne na kawo waman matsayi, wato na zayyane, zayyane da gine-gine, muna shiga daji mu yi aiki, kuma babu takura.
Hada aiki da rayuwar aure:
A gaskiya ni ba na jin komai game da hada aure da aiki, domin kuwa tun farko na yi tsarin da zai taimaka min wajen tafiyar da