Mataimakan gwamnoni 10 cikin 149 da suka gaji masu gidansu tun daga 1999
Jihar Ekiti ce ta fi yawa inda ta yi mataimakan gwamnoni 7, yayin da Ondo da Legas da Kaduna ke da shida-shida.
Daga 1999 da Nijeriya ta koma kan tsarin dimokuradiyya zuwa 2023, jihohi 36 na kasar nan sun samar da mutanen da ba su gaza 149 ba, wadanda suka rike mukaman mataimakan gwamnonin jihohinsu.
A cikin wannan lokaci, Jihar Ekiti ce ta fi yawa inda ta yi mataimakan gwamnoni bakwai, yayin da Ondo da Legas da Kaduna ke da shida-shida.
- NLC ta ayyana zanga-zangar kwanaki biyu kan tsadar rayuwa
- Basunu: Zuriyar Hausawa da ba sa jin Hausa a Ibadan
Jihohi tara ne suka yi biyar-biyar, yayin da 13 ke da uku-uku.
A cikin wannan adadi, guda 10 ne kawai suka yi nasarar gadar kujerun masu gidansu, yayin da wasu mataimakan gwamnoni 10 kuma suka yi nasarar zama ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa.
Kadan ne daga cikinsu suka ci gaba da siyasa tun lokacin da suka zama mataimakan gwamnonin, inda wasu daga cikinsu aka ma manta da su, sai dai idan wani abu ya taso ko kuma a wasu lokuta a ambace su da matsayin da suka rike, wasu kuwa sun koma rayuwar sirri, suna yin sana’ar da suka sani kafin shigarsu siyasa.
Aminiya ta yi dubi a kan ko wadanne irin ayyuka ne Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan ya dora wa mataimakan gwamnonin.
Sai dai a akasarin lokuta ana ganin su a matsayin abin da ake kira da safaya-taya da ba su da wani takamaiman aiki a hukumance.
Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, a sharhin da ya yi na wani littafi mai suna, “Mataimaki da Mulki a Nijeriya” na tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, “Babu wasu ayyuka na musamman da Tsarin Mulki ya bayyana ga Ofishin Mataimakin Gwamna ko ma Mataimakin Shugaban Kasa.
Kodayake an zabe su a kan tikiti ɗaya, a zahiri suna aiki ne bisa umarnin masu gidansu. “Ba don komai ba ne ake amfani da ma’anar safiya taya ga Mataimakin Gwamna ko Mataimakin Shugaban Kasa, sai don kawai aikinsa zai iya gudana ne idan maigidansa ba ya nan, hakan ma na dan takaitatcen lokaci ne,’’ in ji shi.
Wannan rashin samar da wani aiki ga mataimakan gwamnonin, kamar yadda masu sharhi ke gani, na kawo cikas ga dorewar siyasar tsofaffin mataimakan gwamnoni, wadanda galibinsu sukan tsinci kansu, sun rasa tudun dafawa bayan sun bar kujerar mulki.
Don haka mutane da yawa na ganin cewa, ya kamata a samar da wata cibiya da za ta kai ga samar da kafa Kungiyar Tsofaffin Mataimakan Gwamnoni ta Kasa, wanda hakan kan iya jan hankalin shugabannin siyasa wajen ganin an shigar da matsayin mataimakan gwamnoni a cikin Kundin Tsarin Mulkin Kasa.
Wannan rashin bayyana irin aikin da mataimakan gwamnoni za su yi a Kundin Tsarin Mulki shi ne babban dalilin da ya sa ake ganin mataimakan gwamnonin ba kawai a matsayin safiya taya ba, sun kasance ma tamkar wannan matsayi nasu na je-ka-na-yi-ka ne duk da cewa an zabe su tare da masu gidansu ne.
Da yake karin haske kan wannan batu, fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fagge ya shaida wa Aminiya cewa, “Tsarin mulki ya mayar da su tamkar ‘safiya na tayar mota saboda ayyukansu na hannun masu gidansu ne.’’
Ya ce, wani dalilin da ya sa akasarin mataimakan gwamnoni ake mantawa da su a siyasa da zarar wa’adinsu ya kare, shi ne tsarin da ake bi wajen samun mukamin.
“A mafi yawan lokuta, mataimakan gwamnoni ba zabin Gwamna ba ne. Mafi yawan lokuta, wasu jiga-jigan siyasa ne ke dora wa Gwamna irin wannan dan takara a zahiri.
“Don haka, yawanci sai ka samu da kyar ake gamawa lafiya ko kuma a samu haɗin kai tsakanin Gwamna da Mataimakin, hakan ta sa ba sa samun damar yin wani aiki har wa’adinsu ya kare,” in ji shi.
Akasari irin wannan hadi da yawan masu lura da siyasa na ganin an yi shi ne da manufa guda kawai don samun nasarar lashe zaben Gwamna.
Sun yi imanin cewa, yayin da tsarin mulki ya amince cewa Gwamna da Mataimakinsa su yi hadin gwiwa don samun nasarar lashe zabe, amma sai ya yi shiru kan yadda za su tafiyar da aiki tare.
Farfesa Fagge, wanda tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Nazarin Kimiyar Siyasa ta Kasa (NPSA) ce, ya kuma bayyana cewa, saboda wasu gwamnonin na tsoron kada mataimakansu su gaje su, suna yin duk mai yiwuwa wajen mayar da su tamkar saniyar ware a lokacin da suke kan mulki, ta yadda wasu mutane ma ba su sani sunan Mataimakin Gwamnan jihar su.
Galibin gwamnoni na kin sakar wa mataimakansu dama ce, saboda suna jin tsoron kada idan mataimakan suka karbi ragamar mulki daga hannunsu su rama irin mu’amalar da suka yi musu.
A irin wannan yanayi, ba a bai wa mataimakin damar yin wani abu mai muhimmanci da zai sa ya zama tauraro a wajen al’umma.
Ya kara da cewa, “Tsoron gwamnonin ba za su iya juya mataimakansu ba, idan suka ba su mulki, shi ma zai iya zama dalilin da ake ganin yawancin mataimakan ba sa sumun nasarar gadar masu gidansu a lokacin da suka bar mulki.
Aminiya ta gano cewa, mafi yawan ’yan siyasa a yanzu suna ganin gara a nada su a matsayin kwamishinoni saboda mukamin ya fi dama a kan a dauke su a matsayin mataimakan gwamnoni, musamman idan aka nada su kwamishina a ma’aikatar da ake ganin tana da gwabi.
Wannan a mafi yawan lokuta, an ce shi ne dalilin da ya sa mafi yawan mataimaka a koyaushe ke neman a ba su kula da wata ma’aikatar saboda rashin aikin da ofishin Mataimakin Gwamna ke da shi.