Mataimakan Sufeto Janar hudu da kwamishinonin ’yan sanda 17 na fuskantar tuhuma kan rashin da’a

Mataimakan Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya hudu da kwamishinoni 17 na cikin manyan jami’an ’yan sanda 195 da suke fuskanar ladabtarwa kan ayyukan rashin da’a, kuma ana iya yi musu korar kare idan laifi ya tabbata a kansu.Mahukuntan ’yan sandan ne suka bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata, inda suka ce sauran […]

Mataimakan Sufeto Janar hudu da kwamishinonin ’yan sanda 17 na fuskantar tuhuma kan rashin da’a
Mataimakan Sufeto Janar hudu da kwamishinonin ’yan sanda 17 na fuskantar tuhuma kan rashin da’a

Mataimakan Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya hudu da kwamishinoni 17 na cikin manyan jami’an ’yan sanda 195 da suke fuskanar ladabtarwa kan ayyukan rashin da’a, kuma ana iya yi musu korar kare idan laifi ya tabbata a kansu.
Mahukuntan ’yan sandan ne suka bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata, inda suka ce sauran wadanda suka gurfana a gaban Kwamitin Ladabtarwa na Rundunar ta kasa sun hada da na’iban kwamishina hudu da mataimakan kwamishina shida da sauran wadanda suke kan mukaman manyan sufurtanda da mataimakan sufurtanda kamar yadda shugaban kwamitin Sulaiman Fakai ya shaida wa manema labarai a Abuja.
Ana yawan zargin jami’an ’yan sanda da wuce gona da iri ciki har da kashe jama’a da kwace da cin hanci, zarge-zargen da mahukuntansu ke yawan musantawa.
Sulaiman Fakai wanda Na’ibin Sufeto Janar ne bangaren mulki, ya ce tuhumce-tuhumcen da ake wa jami’an sun hada da rashin da’a da rashin ladabi da yin amfani da iko ba bisa ka’ida ba. Sauran suna iya hadawa da kashe jama’a ba tare da gaba
tar da su a gaban kotu ba, da kwace da sata da fashi da makami, a cewarsa. Kuma ya ce, duk wanda aka samu da laifi za yi masa korar kare tare da gabatar da shi gaban shari’a. Sai  dai ya ce, jami’an da aka tuhuma da kisan kuskure ko na gilla ana iya mayar da su aiki, “Idan wata kotu ta nemi a mayar da su bayan ta wanke su.”   
Fakai, ya ce dukkan tuhumce-tuhumce 195 da ke gaban kwamitinsa za a yanke shawara a kansu daga ranar Litinin din zuwa yau Juma’a. “Jami’an da za su gurfana a gaban kwamiin sun hada da Mataimakan Sufeto Janar hudu da kwamishinoni 17 da na’iban kwamishinoni biyu da mataimakan kwamishinoni shida. Laifuffukan da ake tuhumarsu sun hada da rashin da’a da rashin ladabi da wuce gona da iri yayin gudanar da aiki wadanda suna iya jawo kora ko rage mukami ko gargadi ko ritayar dole,” inji shi.
Fakai ya ce jami’an da aka kasa tabbatar da laifi a kansu za a wanke su, yayin da wadanda aka same su da laifi za a ba da shawarar a hukunta su.
Ya ce daga Janairu bara zuwa Yunin bana an yanke shawara kan tuhumce-tuhumce dubu uku, inda aka yi korar kare wa kwamishina daya da mataimakin kwamishina da babban sufurtanda da mataimakan sufurtanda takwas, yayin da aka yi wa kwamishinoni biyu da mataimakan sufurtanda 13 ritaya. Sannan aka rage mukami ga na’ibin kwamishina daya da manyan sufurtanda uku da mataimakan sufurtanda bakwai da na’ibin sufurtanda daya.