Mataimakin dan takara: PDP ta sake shiga tsaka-mai-wuya
Har yanzu bia ga dukkan alamu tsugune ba ta kare ba a jam’iyyar
- ‘Zabar Okowa na iya jawo faduwar PDP’
- PDP ta kafa kwamitin ganawa da Wike
- Wike ya ki ganawa da jakadan Atiku a Turkiyya Ku kwantar da hankalinku — Atiku
Ga dukkan alamu tsugunne ba ta kare ba ga babbar jam’iyyar adawa ta PDP bayan da ta sake samun kanta a tsaka-mai -wuya, kan wanda zai taka wa Atiku Abubakar baya a zaben 2023.
Atiku dai ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin wanda zai dafa masa, sai dai Atiku da Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Dokta Iyorchia Ayu suna fama da matsin lamba kan rikicin da wannan zabi ya haifar a jam’iyyar.
A ranar Juma’ar da ta gabata tsohon Gwamnan Jihar Filato, Sanata Jonah Jang ya yi gargadin cewa jam’iyyar na iya shan mummunan kaye a zaben badi, idan ta gaza daukar matakin gyara don ceto ta daga mummunan halin da take ciki.
Gargadin na Sanata Jang ya zo ne wuni biyu bayan Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom ya nuna damuwa kan yadda Atiku ya ki aiki da matsayar PDP ta ya dauki Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike a matsayin Mataimakinsa Ortom ya bayyana haka ne a daidai ranar da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya rubuta a shafinsa na Tiwita cewa kujerar Shugaban kasa ta Kudu ce bayan karewar wa’adin Shugaba Buhari, inda ya zargi PDP da keta tsarin mulkinta na karba-karbar a tsakanin Kudu da Arewa.
Wasu majiyoyi sun ce manyan ’ya’yan PDP sun fusata kan zaben Okowa da Atiku ya yi, kuma cikin masu fushin har da wasu gwamnonin PDP.
Majiyoyin sun ce wadansu daga cikin gwamnonin sun fara kiran Atiku ya ajiye Okowa ya dauki Wike wanda ya samu kuri’a 14 daga cikin 17 na wakilan kwamitin da jam’iyyar ta kafa don zabo wa Atiku Mataimaki.
Wata majiyar jam’iyyar ta ce, “A daukacin makon jiya, jigajigan jam’iyyar sun yi ta shiga-dafita a sakatariyar PDP ko kiran waya don nuna damuwarsu game da karuwar nuna rashin jin dadi daga wasu gwamnonin jam’iyyar da jiga-jiganta ta yiwuwar faduwa a zaben 2023, inda suke kiran a gaggauta daukar matakin samar da maslaha.
Wata majiya ce, “An gana a tsakanin manyan shugabannin jam’iyyar a Abuja a wannan mako. Kuma Shugaban Kwamitin Amintattu (BoT) ne ya shirya ganawar. Babban abin da aka tattauna shi ne a fara tuntuba don neman afuwar dukkan wadanda aka fusata.”
Ta ce baya ga tuntubar Wike da magoya bayansa, za a bukaci Atiku da Ayu su tattauna da ’ya’yan jam’iyyar da aka fusata don tabbatar da PDP ta shiga zabe na gaba a dunkule.
“Baya ga daukar Okowa a matsayin mai dafa wa Atiku baya, akwai kuma matsalolin da suka taso kan batun wadanda za su tsaya wa jam’iyyar takara a jihohin Osun da Delta da Legas da Ogun da sauransu.
Sai dai kasancewar manyan shugabanni PDP ba sa kasar a yanzu, ya jawo tsaiko kan daukar mataki daga manyan shugabanni. Wike da Atiku da Ayu dukkansu ba sa kasar nan a yanzu da muke magana,” inji majiyar.
Sai dai majiyoyi da dama sun ce zai yi matukar wahala a jingine Okowa a dauki Wike.
Zabar Okowa na iya jawo faduwar PDP – Jang
Sanata Jang wanda dan Kwamitin Amintattun PDP (BoT) ne, ya ce akwai babban aiki a gaban jam’iyyar kafin ta magance matsalar da zaben Okowa da Atiku ya yi ta haifar, sabanin matsayar kwamitin da jam’iyyar ta kafa.
Sanata Jang ya fada wa manema labarai a Jos cewa, hazo ya lullube damar jam’iyyar ta samun nasara a zaben 2023 matukar ba a hanzarta warware rikicin da dauko Okowa da Atiku ya yi a matsayin mai dafa masa a zaben cikin gaggawa ba.
Ya ce, sakamakon zaben Jihar Ekiti na watan jiya sako ne a fili ga PDP cewa ba zai yi mata kyau ta fuskanci zaben badi a rarrabe ba.
Ya ce kasancewarsa cikin wadanda aka kafa jam’iyyar da suke raye ba zai ga abin da zai illata ta ya yi shiru ba.
Ya ce, zaben fid-da-gwani na jam’iyyar ya zo ya wuce an samu dan takara, “Amma abu ne mai bata rai yadda aka zabi mataimakin dan takarar wanda ba komai ba ne face tantagaryar keta ka’ida. Duk muna sane da cewa jam’iyya ta hanyar tuntuba da dan takarar Shugaban kasar ta kafa kwamiti kuma ya zakulo wanda zai dafa masa. A komo daga baya a yi watsi da sakamakon aikin kwamitin cikakkiyar shaida ce cewa ko dai ba a yaba aikin kwamitin ba, ko kuma an nuna ba ya ma da amfani.
Gwamna Samuel Ortom, mamba ne na kwamitin mutum 17 na PDP da suka yanke shawara kan mataimakin dan takarar Shugaban kasar, Jang ya ce, “Goma sha hudu daga cikinmu sun ce a ba Nyesom Wike, amma abin mamaki sai Atiku ya dauki Ya ce: “Ba za ka yi watsi da matsayar kwamitin da kai da kanka ka kafa ba kuma ka sa ran mutane su yi farin ciki. Wadannan mutane da jam’iyyar ta yi wa haka wata manuniya ce cewa akwai jan aiki a gaba. Babu wanda ya shirya wa yakar APC wadda ta gaza a kan alkawuranta kuma take bunkasa a kan farfaganda kuma ya je da rarrabuwar kai. Hakan na nuna cewa lallai ne jam’iyya ta canja tafiya ta ceto mummunan halin da take ciki cikin kankanin lokaci.”
Sanata Jang ya bukaci Kwamitin Amintattu da Kwamitin Gudanawar PDP su yi duk abin da ya wajaba wajen dakatar da ce-ce-ku-cen da ke karuwa kan yadda aka tozarta manyan ’ya’yan jam’iyyar musamman Gwamna Nyesom Wike.
Ya ce halin da ake ciki inda gwamnonin jam’iyyar suka nesanta kansu daga harkokin jam’iyyar da kuma yadda manyan ’ya’yan jam’iyyar suke nuna bacin ransu a fili ba alheri ba ne ga PDP.
Laifin shugabannin jam’iyya ne – Bafarawa
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya dora alhakin rikicin ne a kan shugabannin jam’iyyar, inda ya ce zai zamo hadari ga PDP ta yi watsi da Wike a daf da zaben 2023.
Ya bukaci Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa ya sauka idan ba zai iya magance rikicinta ba.
Bafarawa ya shaida wa manema labarai cewa abin da mutane suke gani a matsayin rikici za a magance shi a sulhun da ke gudana, inda ya ce batun zaben 2023 ya tashi daga kan dan takarar Shugaban kasa shi PDP kadai.
Yana sharhi ne kan kalaman Ortom da aka ruwaito yana cewa Atiku ya wulakanta Wike bayan ya ci zaben fid-da-gwani.
Bafarawa ya ce, “Wannan babbar matsala ce da babu wanda zai yi wasa da ita, sai dai abin takaici wannan rikici shugabannin jam’iyya ne suka haifar. Abin da nake cewa, shi ne dan takarar ya tashi daga mai neman yin takara. Shi dan takara ne, jam’iyya ce ya kamata ta rika juya shi.”
Bafarawa ya ce, “Ba na dora wa kowa laifi in ban da shugabannin jam’iyya, saboda ya kamata su gaggauta magance matsalar.”
Ya ce idan akwai matsala a tsakanin Wike da Shugaban, ya kamata a matsayinsa na Shugaban Jam’iyya na kasa ya mance da haka, ya dauki matakan ceto jam’iyyar saboda shi ne shugaba, kuma aikin da aka ba shi ke nan.
“Idan ba zai iya magance matsalar ba, kawai ya sauka. Amma babu wanda zai yi wasa da Wike babu wanda zai yi watsi da Wike,” inji shi.
Wike ya ki ganawa da jakadan Atiku a Turkiyya
Jaridar Premium Times ta ruwaito a ranar Lahadi cewa Gwamna Wike wanda ke hutu a Istanbul na kasar Turkiyya ya ki ganawa da Alhaji Adamu Maina Waziri wani na hannun damar Atiku Abubakar da ya aike shi don tattaunawa kan yadda za a magance sabaninsu.
Wike ya ki cewa uffan tun lokacin da Atiku ya ki daukarsa mataimakinsa, duk da cewa abokansa ciki har da Gwamna Ortom sun fito fili sun la’anci abin da aka yi masa.
Tura jakada zuwa Turkiyya shi ne yunkurin Atiku na bayan nan don warware takaddamar amma sai Wike ya ki amincewa da bukatar su gana su biyu don isar masa da sako daga Atiku.
Bayanai sun ce bangaren Wike sun gidaya sharadin ‘Lallai Ayu ya sauka’ kafin su goyi bayan Atiku, sai dai majiyoyi sun ce Atiku ya tsaya kai da fata cewa wajibi ne shugaban ya tsaya kan mukaminsa don ya jagoranci kamfe dinsa a zaben na badi, inda bangaren Atikun suka ce Ayu zai sauka ne kawai bayan zaben.
Akwai bayanan da suka ce manyan ’ya’yan PDP suna ta kamu kafar Wike ya sulhunta da Atiku, inda Sanata Bukola Saraki kejagoantar masu kamun kafar Wike don ganin an sulhunta.
Ku kwantar da hankali – Atiku
A wani labarin Alhaji Atiku ya ce duk da rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi, bai ga “wani farrakakken gida ba.”
Ya bukaci ’ya’yan jam’iyyar da kada su fitar da rai daga shirin ceto Najeriya.
Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aike ga kafafen watsa labarai a ranar Lahadi, inda ya ce yana daga cikin halayen dimokutadiyya iya warware rikice-rikicen da ka iya tasowa.
Ya ce, “A matsayin shugabanni da masu ruwa-datsaki a Jam’iyyar PDP, muhawarar da ake samu a jam’iyyarmu manuniya ce kan kasancewarmu jam’iyyar dimokuradiyya. Duk irin muhawarar da muke yi ina da yakinin ana yi ne don dalilai na son bunkasar jam’iyyarmu da kuma kasarmu. Don haka ba na ganin rarrabuwa ce a Jam’iyyar PDP. Ina ganin dama ce gare mu ta mu hada karfi mu dunkule.”
Ya ce, “A matsayina na dan takarar Shugaban kasa na PDP, zan tabbatar da na yi duk abin da zan iya wajen hada kan ’ya’yan jam’iyyar a karkashin lema guda.”
PDP ta kafa kwamitin ganawa da Wike
Don magance rikicin, PDP ta kafa kwamitin sulhu da zai ziyarci Gwamnan na Ribas.
Shugaban Kwamitin Amintattun PDP, Sanata Walid Jibrin ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda ya gargadi ’ya’yan jam’iyyar kan su kame bakunansu daga kalaman da za su dada jefa jam’iyyar a cikin rikici.
Kwamitin a karkashin Atiku ya kunshi Okowa da Ayu da Kwamitin Gudanarwarsa da Jibrin da wakilan BoT da gwamnoni da tsofaffin gwamnoni da ministocin PDP da wasu shugabannin jam’iyyar daga shiyyoyi da jihohi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai taken “Bayanin Shugaban Kwamitin BoT na PDP Sanata Walid Jibrin kan halin da PDP ke ciki.”
Sanarwar ta ce da zarar Atiku da Ayu sun dawo daga waje za su kai ziyara ga Wike wanda babban jigo ne a jam’iyyar kuma mai biyayya wanda ya taimaka sosai wajen gina jam’iyyar don haka zai su roke shi kada ya bar jam’iyyar.