‘Mataimakin Direban jirgin saman Jamus ne ya haddasa hadarin jirgin da gangan’

A jiya Alhamis ne babban mai gabatar da kara Brice Robin ya ce mataimakin matukin jirgin saman kasar Jamus ne ya haddasa hadarin jirgin da gangan, bayan ya karkata akalar jirgin zuwa tsaunukan yankin Alps na kasar Faransa, mai cike da hadari. Mista Robin ya bayyana hakan ne bayan sauraron wani faifan muryar abubuwa da […]

‘Mataimakin Direban jirgin saman Jamus ne ya haddasa hadarin jirgin da gangan’
‘Mataimakin Direban jirgin saman Jamus ne ya haddasa hadarin jirgin da gangan’

A jiya Alhamis ne babban mai gabatar da kara Brice Robin ya ce mataimakin matukin jirgin saman kasar Jamus ne ya haddasa hadarin jirgin da gangan, bayan ya karkata akalar jirgin zuwa tsaunukan yankin Alps na kasar Faransa, mai cike da hadari.

Mista Robin ya bayyana hakan ne bayan sauraron wani faifan muryar abubuwa da suka faru a cikin jirgin gabanin faruwar hadarin, inda ya zargi mataimakin direban da kulle kansa shi kadai kuma ya hana direban jirgin dawo cikin wurin da ake kebe masu domin gudanar da aikinsu. Ya kara da cewa daga nan ne sai mataimakin direban ya ci gaba da tukin jirgin shi daya.
Shugabannin kasashen Faransa da Spain da kuma Jamus sun ziyarci tsaunukan Alps da ke Faransa, wurin da jirgin saman kasar Jamus ya fadi ranar Talata, inda aka yi amannar cewa mutane 150 ne suka rasa rayukansu.
A lokacin ziyarar, shugabannin sun gana da ‘yan ‘uwan wadanda hadarin jirgin saman, samfurin Airbus A-320 ya halaka.
A halin da ake ciki dai jiragen saman helikwabta suna ci gaba da neman gawawwaki duk da ruwan sama da dussar kankara da aka fara samu.
Ministan al’amuran cikin gidan kasar Faransa, Bernard Cazeneube, ya ce na’urar da ke nadar murya a cikin jirgin ta lalace. Sai dai duk da haka, ya ce na’urar za ta samar da bayanan da masana kan jirgin sama za su yi amfani da su domin gano dalilin da ya sa jirgin ya fadi.
Har ila yau, jami’ai sun yi gargadin cewa za a kwashe kwanaki da dama kafin a gano gawarwakin mutanen da suka mutu a cikin jirgin saboda rashin kyawun yanayi.
Jirgin mallakin kamfanin Germanwings yana kan hanyarsa ce ta zuwa birnin Duesseldorf na kasar Jamus daga birnin Barcelona na kasar Spain, lokacin da hadarin ya faru.
Kuma a yau Juma’a kasar Spain take kammala makokin kwana uku da Firaministan kasar Mariano Rajoy, ya bayyana ranar da jirgin ya fadi domin tunawa da ‘yan kasar su 45 da ke cikin jirgin.