Mataimakin fasto ya kashe shi a saman mimbarin coci

Lekan Ogundipe ya kashe limamin cocin tare da kona gawarsa a saman mumbarin cocin a Jihar Osun.

Mataimakin fasto ya kashe shi a saman mimbarin coci

Wani mataimakin limamin coci Lekan Ogundipe ya kashe limamin cocin tare da kona gawarsa a saman mumbarin cocin a Jihar Osun.

Lamarin ya afku ne a yammacin ranar Litinin lokacin da limamin cocin na Celestial Church of Christ, Evangelist Moris Fadehan, ya koma yin addu’a a cikin cocin da ke garin Ile-Ife da ke  jihar.

Ana zargin Ogundipe ya kai masa hari ne da wukake da kusoshi, inda ya rika caka masa wuka, bayan da farko ya buge shi da kararrawa.

Hakan na zuwa ne bayan dambarwar cin zarafi da mataimakin limamin cocin ya yi wa wata malamar cocin a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya haifar da rashin jituwa tsakanin limamin cocin da mataimakin nasu.

“Na baya-bayan nan akwai cin zarafin da Lekan ya yi wa wata malama a cocin a makon jiya; na amince, amma ya ce zai dauki matakin bayan ya tattauna da dattawa.

“Ranar Litinin da yamma ina shirin cin abinci sai ga Lekan ya zo ya ce min wuta na ci a jikin mamacin kuma ba shi da rai a kasa.

“Muka tafi tare da shi da kuma matata zuwa cocin inda muka tarar da gawar mamacin da aka kona a cikin cocin a saman mimbari.

“Mun gano jini da yanka a sassa daban-daban na jikinsa, da muka tambaye shi yadda ya same su, sai ya yi yunkurin gudu, amma muka kama shi muka kulle a motata sannan muka kira ’yan sanda.

“Da akwa bude gawar marigayin, sai aka ga kunnensa da wasu sassan cikinsa da yanka, sannan an buga masa kusa a kunne.

“Daga bisani an kai gawar zuwa dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife.

“Lekan ya shaida wa ’yan sanda cewa shi ne ya aikata laifin saboda sabaninsu da marigayin.”

Malamar da ake batu bayyana cewa: “Wanda ake zargin ya kai mani hari a makon jiya lokacin da na ce masa ya daina gaya wa ’yan uwa cewa muna da soyayya da shi, Fasto Fadehan bai ji dadin lamarin ba, har ya gargadi Lekan game da yin hakan a cocin.”

Kakakin ’yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da kama Ogundipe, kuma an ajiye gawar Fasto Fadehan a dakin ajiyar gawarwaki domin gudanar da bincike.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta