Mataimakin Gwamnan Jigawa ya yi barazanar ajiye mukaminsa?
Wata majiya mai karfin gaske ta ce Mataimakin Gwamnan jihar zai sauka daga mukaminsa saboda ba a yin komai da shi, abin da wasu suka ce an mayar da shi tamkar ‘safaya taya.’ Kamar yadda binciken Aminiya ya kalato, majiyar ta ce sau uku Mataimakin Gwamnan yana yunkurin ajiye mukamin nasa amma masarautar Hadeja ta […]
Wata majiya mai karfin gaske ta ce Mataimakin Gwamnan jihar zai sauka daga mukaminsa saboda ba a yin komai da shi, abin da wasu suka ce an mayar da shi tamkar ‘safaya taya.’
Kamar yadda binciken Aminiya ya kalato, majiyar ta ce sau uku Mataimakin Gwamnan yana yunkurin ajiye mukamin nasa amma masarautar Hadeja ta hana shi ajiyewa. Saboda a cewar majiyar tamu, mai martaba sarkin na Hadeja ne ya ce matakin da mataimakin gwamnan ke kokarin dauka na ajiye mukaminsa ya yi gaugawa, bai kamata ya ajiye aiki yanzu ba, kamata ya yi ya bari a sake turawa kadan; watakila a sami gyara a cikin tafiyar
Da yake mayar da jawabi a kan al’amarin, Kwamashinan Watsa Labarai na jiha. Alhaji Bala Ibrahim Mamsa, ya ce maganar da ake bazawa a gari a kan cewa Mataimakin Gwamna zai ajiye mukaminsa ba gaskiya ba ne, yarfe ne irin na ’yan adawar siyasa, wadanda ba su son zaman lafiya, sai haddasa fitina.
Ya kara da cewa masu maganar cewa mataimakin ya yi kokarin ajiye aikinsa har sau uku, suna son haifar da rudani ne kawai, domin kawai su kawo cikas a cikin tafiyar da ake yi a Jihar Jigawa.
Kamr yadda ya ce, babu wata matsala tsakanin gwamnan da mataimakinsa; lafiya kalau suke zaune, babu maganar jingine mataimakin gwamnan a gefe, kamar kayan wanki.
Wakilin Aminiya ya tuntubi fadar mai martaba Sarkin Hadeja ta waya, inda Alhaji Maina Kawu, tsohon Sakataren Sarki ya musanta cewa Sarkin Hadeja ya shawarci mataimakin gwamna game da yunkurinsa na aje mukami. “Na yi mamakin labarin kuma na yi takaicin yadda mutane suke sha’awar baza karya marar tushe domin cin ma burinsu na siyasa alhalin karya ne. Yaushe aka yi gwamnatin har da za a ce an fara samun matsala?” Inji shi.
Kamar yadda bincike ya nuna, ba tun yau ba ake baza irin wadannan labarun a Jihar Jigawa. A farkon zuwan wannan gwamnatin ma, wasu sun yada jita-jitar cewa wasu daga cikin masu bai wa gwamna shawara sun raina mukaman da aka ba su, za su ajiye aikinsu. Hatta Shugaban jam’iyyar APC na jihar da mai ba gwamna shawara a kan harkokin watsa labarai, an ce sun yi barazanar ajiye mukamansu saboda wai gwamnatin ba ta tafiya a kan daidai kamar yadda suke tunani. Sai dai tun a wancan lokacin, wadannan jami’ai suka musanta faruwar haka.