Mataimakin gwamnan Jihar Enugu zai kalubalanci tsige shi

Ranar Talata ’yan majalisar dokoki ta Jihar Enugu suka yi ittifakin tabbatar da tsige Mataimakin gwamna, Mista Sunday Onyebuchi, saboda samunsa da laifukan yin kiwon kaji a kusa da gidan gwamnati da kuma kin wakiltar Gwamna Sulliban Chime sau biyu.Wakilan majalisar su 24 suka tabbatar da tsigewar bayan da suka yi na’am da rahoton kwamitin […]

Mataimakin gwamnan Jihar Enugu zai kalubalanci tsige shi
Mataimakin gwamnan Jihar Enugu zai kalubalanci tsige shi

Ranar Talata ’yan majalisar dokoki ta Jihar Enugu suka yi ittifakin tabbatar da tsige Mataimakin gwamna, Mista Sunday Onyebuchi, saboda samunsa da laifukan yin kiwon kaji a kusa da gidan gwamnati da kuma kin wakiltar Gwamna Sulliban Chime sau biyu.
Wakilan majalisar su 24 suka tabbatar da tsigewar bayan da suka yi na’am da rahoton kwamitin mutum bakwai da aka kafa don binciken zargin da ake yi Mista Sunday, alhalin sun dogara da sashe na 188, karamin sashe na 9 na kundin tsarin mulki.
A yayin da yake tsokaci dangane da tsigewar da aka yi masa, mataimakin gwamnan ya ce bai yi mamakin yanayin yanke hukuncin ba, kodayake zai kalubalance shi a kotu tunda ba wata hujja tabbatacciya kan aukuwar laifukan da aka zarge shi da su.
Ya sanar da manema labarai cewa bai gamsu da bayanin kwamitin binciken ba, musamman ma da yake an tsige shi ne a ranar da Babban Jojin jiha, Mai shari’a Innocent Umezulike ya zabi ’yan kwamitin binciken.  “Hukuncin ’yan kwamitin ne da na majalisa na kashin kansu suka yanke, amma Allah zai yi naSa, wanda ya fi na kowa.  Ban yi zaton a yau (Talata) aka tabbatar da tsige ni ba, ina ganin sun zartar da shi ne tun lokacin da aka kafa kwamitin binciken domin duk an yi abin ne a gamin-gambiza, kuma na sami damar ganin rahoton kwamitin a ranar Litinin da yamma.” Inji shi.