Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna ya bukaci mutanen kudancin jihar su zauna lafiya

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Mista Barnabas Bala Banted ya yi kira ga jama’ar Kudancin Jihar da su kaunaci juna kuma su zauna lafiya don samun zaman lafiya mai dorewa a yankin da ya fito.Mataimakin Gwamnan ya yi kiran ne a wajen walimar buda-baki da aka shirya a tsakanin Musulmi da Kiristocin kudancin jihar, wanda aka […]

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna ya bukaci mutanen kudancin jihar su zauna lafiya
Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna ya bukaci mutanen kudancin jihar su zauna lafiya

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Mista Barnabas Bala Banted ya yi kira ga jama’ar Kudancin Jihar da su kaunaci juna kuma su zauna lafiya don samun zaman lafiya mai dorewa a yankin da ya fito.
Mataimakin Gwamnan ya yi kiran ne a wajen walimar buda-baki da aka shirya a tsakanin Musulmi da Kiristocin kudancin jihar, wanda aka gudanar a masaukin baki na Sakatariyar karamar Hukumar Jama’a da ke Kafanchan, inda bayan buda-bakin aka ba jama’a damar yin tambayoyi da gabatar da korafe-korafen da ke damunsu.
 A lokacin amsa tambayoyin, Mista Bala Banted ya fayyace musu abubuwa daki-daki da suka shafi gwamnatinsu ciki har da rashin biyan dagatai da hakimai albashi na tsawon lokaci, inda ya ce maganar albashin dagatai alhaki ne na kananan hukumomi, kuma saboda karyewar farashin man fetur a kasuwannin duniya da rage adadin man da ake fitarwa daga ganga miliyan biyu zuwa miliyan daya da ’yan kai sai hakan ya shafi kudin shiga na tarayya da jihohi da kananan hukumomi kuma hakan ya haifar da kasa biyan albashin ma’aikata har ya gangaro kan dagatai da hakimai.
Mista Banted ya kuma ce tantance ma’aikata da ake yi a kananan hukumomi ya samu kafar ungulu daga marasa kishi inda maimakon su cire ma’aikatan bogi sai suka koma suna kokarin cire na zahiri. Mataimakin Gwamnan ya ce sakamakon tantance ma’aikata ne aka gano ma’aikatan boge har gwamnati take iya biyan ma’aikata albashi, inda a baya take kashe Naira biliyan 2 da miliyan 700, inda a yanzu ya dawo Naira biliyan 2 da miliyan 200, alhali kudin shigar da gwamnatin jihar ke samu yanzu bai wuce Naira biliyan 2 da miliyan 400 ba.
Alhaji Sama’ila Barau Maigoro, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC a Kudancin Kaduna, ya bayyana wa wakilinmu farin cikinsa kan wannan hobbasa da kuma shirya buda-bakin da ya kusanto da talakawa ga gwamnati don jin koke-kokensu da samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista.
Mahalarta taron sun nuna gamsuwa da jin dadi a kan wannan taron da ba a taba shirya musu irinsa a baya ba.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe